1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

150410 Papst Dialog Religionen

April 18, 2010

A wannan Litinin aka cika shekaru biyar daidai da aka zaɓi Joseph Ratzinger ɗan Jamus, a matsayin shugaban Cocin Roman Katholika na duniya.

https://p.dw.com/p/MziW
Paparoma Benedikt na 16 bayan an zaɓe shi a matsayin PaparomaHoto: AP

Tun daga wannan rana ne kuma ya zama Paparoma inda ya ke amsa sunan Benedikt na 16. A lokacin jama'a ta yi matuƙar murna, to amma da tafiya ta yi tafiya sai farin jininsa ya fara raguwa a tsakanin jama'a. Yanzu haka dai yana shan suka kan yadda ya tinkari batun lalata da yara. To sai dai ba a nan ta tsaya ba domin Paparoman na ƙara shan suka saboda rashin iya ma'amala da mabiya addinan Musulunci da Yahudanci.

Ko masu sukar lamirinsa a cocin Katholika suna yabawa Benedikt na 16 da kyakkyawar niyar tuntuɓar juna tsakanin addinai. Ganin tun a cikin shekara guda da ya zama Paparoma, Bajamushen ya ta da hankalin dukkan duniyar musulmi, wani masanin addini na ƙasar Switzerland Hans Küng ya bayyana hakan da cewa tuntuɓen harshe ne. Wasu kuma na masu ra'ayin cewa ba a bawa Paparoman shawara mai kyau ba. Shi dai Paparoma Benedikt na 16 a wani jawabi da yayi a garin Regensburg a cikin watan Satumban shekarar 2006 yayi wani furuci da ya ɓata ran Musulmai. Jim kaɗan bayan haka shugabannin Musulmai a ko-ina cikin duniya sun aikewa da Paparoma wata buɗaɗɗiyar wasiƙa suna kira gareshi da ya janye wannan furuci. Shugaban ƙungiyar Turkawa Musulmi a Jamus Bekir Alboga, ɗaya daga shugabannin tattaunawar samun fahimtar juna tsakanin addinai a Jamus, a hira da DW ya yi kira ga Paparoma kamar haka.

Prince Ghazi bin Mohammed Papst Benedikt XVI Jordan
Hoto: AP

"Abin baƙin ciki ne da waɗannan kalaman suka fito daga bakin babban wakilin fadar Vatikan. Ina fata Paparoma zai hanzarta yin gyara kuma ya nemi gafarar Musulmai. Ina kuma fata zai tsaya tsayin daka ga shirin Vatikan na tattaunawa da sauran addinai."

Vatikan ta yi mamakin yadda aka yi ta zanga-zanga tare da tashe tashen hankula, tana mai cewa an yiwa Paparoman mummunar fahimta. Makonni ƙalilan baya, Benedikt na 16 ya samu nasara a ƙoƙarin ɗinke wannan ɓaraka. Ya kai ziyara a wani masallaci da akewa laƙabi da "Shuɗin Masallaci" a birnin Istanbul na ƙasar Turkiya, inda ya gana da babban limamin masallacin kuma suka yi addu'o'i tare. Ya jaddada dangantaka tsakani Musulunci da Kiristanci.

"Yanzu dai ya zama dole Musulmai da Kiristoci su bi hanyoyin da addinansu suka umarce su kana kuma su amince da juna, musamman saboda matsalolin da kan taso sakamakon rashin fahimtar tarihin kyakkyawar dangantaka tsakaninsu."

Papst Benedikt XVI. in Israel
Hoto: AP

Benedikt na 16 ya kuma tabƙa wani kuskuren a tattaunawa da Yahudawa wadda aka fara akan kyakkyawar turba. Jim kaɗan bayan ya zama Paparoma, ya kai ziyara wurin ibadar Yahudawa a birnin Kolon inda ya ba da tabbacin ƙarfafa aniyarsa ta kyautata dangantaka da al'ummar Yahudawa.

To amma shekara guda bayan haka ya tabƙa wata katoɓarar a cikin wata addu'a dake cewa Allah Ya haskaka zukatan Yahudawa domin su amince da Issah Almasihu a matsayin mai ceto. Wannan tamkar cin fuskata ne ga Yahudawa. Wani abin kuma shi ne a bara lokacin da Paparoman ya ɗage haramci akan wasu bishop-bishop guda huɗu ciki har da Richard Williamson wanda ya ƙaryata aukuwar kisan ƙare dangi da aka yiwa Yahudawa. Paparoma ya bayyana wannan lamarin da cewa kuskure ne daga mashawartansa.

A cikin shekaru biyar a matsayin Paparoma, rashin fahimta, da kurakurai da tuntuɓen harshe da suka yi illa ga shirin Benedikt na 16 na tuntubar juna da Musulunci da Yahudanci, ana iya cewa da sauran aiki a gabansa.

Mawallafi: Klaus Dahmann/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi