1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyu da kashe Osama Bin Laden

May 2, 2013

A cikin watan Mayu na shekarar 2011 wata tawagar rundunar sojojin sirri na Amurika ta jagoranci farmakin da ya hallaka shugaban ƙungiyar Al-Qaida a Abottabad da ke a Pakistan inda ya ɓuya.

https://p.dw.com/p/18QbT
** FILE ** This undated photo shows al-Qaida leader Osama bin Laden in Afghanistan. bin Laden will release a new Internet message that focuses on Iraq and an al-Qaida linked insurgent group, a terrorism monitoring group said Thursday, Dec. 27, 2007. (AP Photo)
Hoto: AP

Da zaran an yi maganar Al-Qaida abu na farko da jama'a suke yin tunani a kansa shi ne hare haren 11 ga watan Satumba, wanda ƙungiyar ta kai a shekarun  2001 akan cibiyar kasuwanci ta duniya wato World Trade Center. Wanda a cikin mutane kusan dubu uku suka mutu kana wasu da dama suka jikata.

Sojojin ƙundunballa na Amurika waɗanda yawan su ya kai kusan 300  sun daɗe suna yin bincike akan iyakar Afaganistan da Pakistan domin farautar Bin Laden ,ko a mace ko a raye , wanda a ƙarshe suka kashe shi  a gidansa da ke a Abottabad a Pakistan.

Ƙarfin ƙungiyar Al-Qaida ya ragu bayan mutuwar Bin Laden

Bayan mutuwar ta Bin laden dai ƙungiyar ta Al-Qaida ta samu rauni kamar yadda Guido Steinberg na wata cibiyar binciken kimiyyar siyasa a nan Jamus ya nunar a cikin wata hirar da tashar DW ta yi da shi.

epa02771862 (FILE) An Ausaf newspaper photograph dated 08 November 2001 shows Saudi-dissident Osama bin Laden (L) sitting with his deputy Ayman al-Zawahiri at his hide out at an undisclosed location in Afghanistan. The United States will regret its killing of Osama bin Laden, al-Qaeda deputy Ayman al-Zawahiri said in a video that surfaced on the internet 07 June 2011. In his first statement since bin Laden was killed on 02 May, al-Zawahiri said, 'Now you rejoice over the martyrdom of Sheikh Osama bin Laden, the holy warrior, but also you will regret it.' In the nearly 30-minute video, he said Washington was happy about the death of Saddam Hussein, but that Iraq then fell into the hands of mujahideen, or holy warriors. It is not clear if he is now the leader of al-Qaeda. EPA/AUSAF NEWSPAPER / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY +++(c) dpa - Bildfunk+++
Bin Laden tare Ayman Al-ZawahiriHoto: picture alliance / dpa

Ya ce:'' Jagoran ƙungiyar na yanzu Ayman Al Zawahiri  ya na daga cikin shugabannin ƙungiyar wanda ake ta yawan yin tsokaci akan su, na rashin samun amanar ya'yan ƙungiyar baki ɗaya.''

A yanzu za a iya cewar magoya bayan ƙungiyar ta Al Qaida a duniya sun kai dubu goma misali, kuma kungiyar ta yaɗu da gaggawa a cikin ƙasashe inda ta ke da rasa, da dama a cewar SteiNberg.

Ya ce :'' A kwai rasa ƙungiyar a Iraki a yankin arewacin Afirka zuwa Aljeriya, da  Somaliya da Libiya da kuma Mali. Ƙungiyar ta samu ƙarin ma'abiya a Iraki inda ta ke da kimanin mutane dubu.''

Ƙasashen duniya na ƙara ɗaukar matakan yaƙi da ta'addanci

An  dai kai ga samun ragowar kai hare hare na ta'addanci a duniya na ƙungiyar  saboda tsattsauran matakan yaƙi da ta'addanci da ƙasashen duniya suka tanada tun bayan hare haren na 11 ga watan Satumba. wani bincike na ƙwarraru ya nuna cewar ƙungiyar ta Al Qaida ta fi kai hare hare a cikin ƙasashen musulumi kana kuma mafi yawanci waɗanda ta ke kashe wa musulumi ne. Musammun ma  dangane da yadda ƙungiyar ta samu kafuwa a cikin ƙasashen larabawa irin su Siriya, da Yemen da Tunisiya.  wanda masana  ke ganin cewar, wata sabuwar dabbara ce, ta jahadi da ƙungiyar ta ke yi a cikin ƙasashen larabawan. Inda magoya bayan ƙungiyar ke kai hare hare na ta'addanci a cikin yankunan su, wanda lamarin ya ƙarfafa a cikin shekaru huɗu na baya baya nan.

US soldiers stand guard at the site of twin suicide attacks in Kandahar on January 6, 2013. Two suicide bombers struck a meeting of community leaders in a southern Afghan town near the Pakistan border on Sunday, killing at least five people and wounding 15, officials said. One gunman on foot opened fire on guards at the entrance of the council building in Spin Boldak, forced his way inside and detonated himself, while a second attacker rammed an explosives-laden vehicle into the outside walls. AFP PHOTO / JANGIR (Photo credit should read JANGIR/AFP/Getty Images)
Sojojin AmurikaHoto: AFP/Getty Images

Dukkanin al'ummomin duniya na yin Allah Wadai da ayyukan ta'addanci

Ba shakka al'ummomin duniya baki ɗaya kama da ga musulumi zuwa ma'abiya addinin krista da ma waɗanda ba su da addini, ko wanne na yin Allah Wadai da lamarin ta'addanci. Kuma ko da shi ke an karya lagon ƙungiyar ta Al -Qaida, tun bayan mutuwar Osama Bin Laden har yanzu dai a kwai buƙatar zage damtse wajan yaƙi da ta'addancin a duniya baki ɗaya.

ARCHIV - Ein Turm des bei dem Terroranschlag von zwei Passagiermaschienen getroffenen World Trade Centers in New York stürzt ein und eine Wolke aus Staub, Rauch und Asche steigt in die Luft (Archivfoto vom 11.09.2001). Osama Bin Laden (undatiertes Archivfoto), der meistgesuchte Terrorist der Welt, ist tot. Das sagte US-Präsident Barack Obama in einer Fernsehansprache am Sonntag (Ortszeit) in Washington. Foto: Hubert Boesl dpa (zu dpa 0116 vom 02.05.2011) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hare haren 11 ga Satumba a cibiyar kasuwancin AmurikaHoto: picture-alliance/dpa

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da kuma Rahoton da Mahammadou Awal Balarabe ya haɗa mana dangane  da yaƙi da ayyukan ta'addanci da ƙasashen duniya suke yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita        : Zainab Mohammed Abubakar