1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru hudu da fara rikicin kasar Siriya

Mahmoud Yahya AzareMarch 15, 2015

A wannan Juma'ar ce ake cika shekaru hudu da fara boren neman sauyi a kasar Siriya, boran da ya rikide zuwa yakin basasar da ya salwantar dubun dubatan rayuka da kuma raba wasu masu yawa da muhallansu.

https://p.dw.com/p/1Eqg9
Syrien Demonstrationen
Hoto: picture-alliance/dpa

A shekarun hudu da suka gabata, daruruwan yan kasar ta Siriya suka bazama kan titunan garin Dir'a suna rera taken neman 'yanci cikin lumana.

Bayan kusan watanni shida da wannan zanga zangar lumanar wacca ta kai ga kashe gwamman mutane a hanun yan bangar siyasa da ake kira Shabbiha da jami'an tsaro, gami da tsare darururwan masu ta da kayar baya, fatalin da masu zanga zangar suka yi da sauye sauyen da gwamnatin Bashar Al Asad ta yi, gami da ci gaba da yin zanga zanga har cikin kwaryar babban birnin kasar Demascus, ya sanya jami'an tsaro gami da sojoji yin rubdugu kan masu zanga zangar da zimmar murkushesu da karfin tuwo.

Syrien Gefechte zwischen Rebellen und Regierungstruppen in Aleppo
Hoto: Z. Al-Rifai/AFP/Getty Images

Wannan mataki da gwamnatin ta Bashar Al Asad ta dauka kan masu neman sauyin wadanda ta ke siffanta su da yan ta'adda da masu barna, ya sanya taken zanga zangar dake neman yanci da mutunci daukar sabon salo, ta yadda ya koma yin kira ga shugaba Bashar din yayi murabus.

Shiga tsakanin da manzanin Majalisar Dinkin Duniya su uku,da kudurorin neman sasantawar da kasashen larabawa suka gabatar, gami da taruka biyu a Geneva da Majalisar duniyan ta dauki nauyin shiryawa don lalubo mafuta ga wannan rikicin da ya rikede zuwa yakin basasa mafi muni a yankin, duk wadannan sun gaza wajen samo bakin zaren warware wannan rikicin da ya zuwa yanzu, Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce yayi sanadiyar asarar rayukan mutane dubu dari biyu da hamsin, gami da raba kusan mutane miliyan sha daya da gidajensu baya ga rugu-rugu da ya yi da fiye da rabin kasar.

Bullar kungiyar IS a kasar ta Siriya,gami da baki yan kasashen waje dake samun tallafin kudadede da makamai daga kasashen Saudiya da Qatar da Emarat da Turkiya wadanda ke neman ganin bayan mulkin Bashar Asad, ya sanya rikicin daukar wani sabon salon bangarancin akida, yadda kungiyoyin masu fafutuka da makamai na Yan shi'a irinsu Hizbullah da sauransu su ka shiga kasar don kare gwamnatin Bashar Al Asad.