1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ko ana samun magudi da murdiya a zaben Jamus?

September 20, 2013

A daidai lokacin da ake cikin hali na zaben majalisar dokokin Jamus, wato Bundestag, mun sami tambayoyi game da ko akan samu, ko akan yi magudin zabe a Jamus.

https://p.dw.com/p/19lEH
Hoto: picture alliance / dpa

Dangane da haka, Klaus Pötzsch, na hukumar zaben kasar ta Jamus yayi bayanin cewa tsari da shirye-shirye da kuma tafiyar da zabe a nan Jamus, al'amura ne da ko wane lokaci sukan kasance an yi su a fili, ba tare da boye-boye ba.

Pötzsch shine mutumin da alhakin shiryawa da tafiyar da zabubbukan taraiya da na Turai ya rataya a wuyansa. A takaice, shine babban jami'in hukumar zabe ta kasa baki daya.

Yace Babban jami'in hukumar zabe ta taraiya shine yake da alhakin tsarawa da tafiyar da zaben taraiya na majalisar Bundestag da zaben majalisar Turai.

Jami'in yace tun kafin zaben, akan shirya a kuma tabbatar da ganin cewar babu wani kuskure da aka samu, babu kuma tangarda da zata samu a lokacin zaben. A ko wace rumfar zabe zabe akan tanadi mataimaka tsakanin mutane takwas zuwa tara. Gaba daya a ranar zabe, akan sami mataimaka masu bada gudummuwa ba tare da an biya su ba misalin dubu 630. A kasar ta Jamus, duk mutumin da akalla ya kai shekaru 18 da haihuwa, yana iya gabatar da kansa a karamar hukumar yankin da yake, domin a dauk shi a matsayin mai taimako a ranar zabe.

Tun kafin a fara kada kuri'a, mataimakan zasu duba su ga ko akwatin zaben wanda a ciki ne za'a rika jefa kuri'u a hakika babu komai cikinsa. A lokacin kada kuri'a kuma, mataimaka sukan tabbatar da ganin duk wanda yazo zabe an tabbatar da ko wanene shi, kuma mai zaben ya nuna shaidar yancinsa na kada kuri'a da aka aiko masa tun kafin ranar zabe.

Mataimaka a rumfar zabe suna tabbatar da ganin duk wanda yazo zabe babu wanda zai matsa lambar yin abin da bai so ba. Misali, idan masu goyon bayan wata jam'iya suka yi kokarin jan hankalin wani ya kadawa jam'iyarsu kuri'arsa, mataimakon sukan hana su yin haka. Tun da farko su kansu mataimakan sai sun yi alkawarin ba zsu nuna son kai a aikinsu ba, ko da shike hakan ba yana nufin mataimakan ba a yarda su zama yan wata jam'iya bane.

Klaus Pötzsch
Shugaban hukumar zabe ta Tarayya Klaus PötzschHoto: Destatis

Da karfe shidda daidai na yamma, akan rufe rumfunar zabe, sa'annan bisa aiki da ka'idar da tun farko aka shimfida sai a fara kidaya kuri'u. Klaus Pötzsch yace:

Kidayar kuri'un abu ne da akan yi shi a bainar jama'a. Akwai ka'idar cewar ko wace kuri'a sai an ambace ta da karfi kuma a fili, an kuma kidaya ta a rubuce. Takardun da dake dauke da lissafin kidayar, wajibi ne shugabannin zaben su amince, su kuma sanya hannu kansu, kafin su mika su zuwa gaba. Wato dai babban abin dake da muhimmanci shine a yi komai a bainar jama'a.

Ta hanyar kula da kuma tsari mai kyau, an dauki matakin ganin babu magudi ko murdiya a zabubbukan Jamus, to amma babu mai iya tabbatar da ba za'a sami wani kurkure nan da can ba. Abu mai rauni a wannan tsari na zabe shine yancin kada kuri'a ta hanyar yin zabe ta wasika dake kara samun farin jini a kasar. A birane da manyan garuruwa akalla kashi 30 cikin dari na zabe akan yi shi ne ta hanyar aikewa da kuri'u ta wasika. Ta wannan hanya, babu mai iya tabbatar da sirin zaben. Tana iya yiuwa mai kula da maras lafiya a sibiti yayiwa cikewa maras lafiya kuri'ar zabe ko kuma miji ya yiwa matarsa. Kazalika a Jamus, kamar a Amirka ko Brazil, an taba tafiyarda zabe ta hanyar amfani da injuna masu kwakwalwa domin kada kuri'u a shekara ta 2005. Daga baya a shekaqra ta 2009 kotun kare tsarin mulki ta tarayya ya soke zaben wannan hanya, bisa dalilin cewar zabe tilas ne a yi shi a bainar jama'a, yadda za'a kaucewa magudi ko murdiyar kuri'u.

Deutschland Wahlhelfer Bundestagswahl 2005 Stimmzettel werden ausgezählt
Mataimaka masu kidaya kuri'u a zaben TarayyaHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Anna Peters/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman