1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin taron Siriya zai kawo karshen zubar da jini a kasar?

January 22, 2014

Ranar Laraba a garin Montreaux aka bude zaman taron sulhun rikicin kasar Siriya, tsakanin gwamnatin kasar ta shugaba Bashar al Assad da kungiyoyin yan tawaye.

https://p.dw.com/p/1AvKf
Hoto: Getty Images

Ranar Laraba a garin Montreaux na kasar Switzerland aka bude zaman taron neman sulhun rikicin kasar Siriya, tsakanin gwamnatin kasar ta shugaba Bashar al Assad da kungiyoyin yan tawaye. Bayan da janar sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya bude taron, wakilan Assad da na yan tawayen sun shiga kace-nace da juna a game da makomar Assad a kasar ta Siriya. Yayin da yan tawayen da magoya bayansu ciki har da Amirka da Saudi Arabiya suke cewar Assad ba zai sake taka rawa a kasar nan gaba ba, Rasha tace bai kamata kasashen ketare su ci gaba da shisshigi a rikicin kasar ba.

To da alamun cewar ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier da gaske yake yi, lokacin da ya baiyana fatan amun nasarar taron na Siriya da aka bude yau, ko kuma watakila ya baiyana fatansa ne saboda kada ya fito fili ya nuna rashin karfin zuciya ga samun nasarar wannan taro. Jim kadan kafin taron abokan Siriya da aka yi a farkon watan Janairu a Paris, Steinmeier yace shekara ta 2014, tana iya zama mai muhimmanci ga yankin baki daya. Yanzu kadan ya rage a cimma yarjejeniya da Iran kan manufofinta na Atom, ga kuma ci gaba a kokarin cimma burin samun kasashe biyu kafada da kafada da juna tsakanin Israila da Palesdinawa, yanzu kuma ga yiwuwar kawo karshen zub da jini a Siriya.

To sai dai lokacin wani jawabi a majalisar dokoki, Steinmeier ya nuna alamun cewar zaman lafiyar Siriya ba zai samu cikin gaggawa yadda ake so ba. Yace har yanzu muna nesa da cimma burinmu na zaman lafiya a Siriya, amma kofar hakan ta dan bude, bayan da aka ja hankalin shugaban kasa Basha al-Assad ya mika makamansa masu guba. Nasarar da aka samu ta karbe makaman masu guba daga Assad ba ma ta hana shiga wani sabon mataki ne a rikicin na Siriya ba, amma har ta kuma kawo karshen babakeren da akai ta samu a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya karon farko tsakanin Amirka da Rasha, wadanda suka hada gwiwar samun kwarya-kwaryar hadin kai kan rikicin na Siriya. To amma ministan ya kara da cewa:

"Ina kuma iya nunarwa kai tsaye cewar fahimtar bukatun duka bangarorin dake rikici da juna a kasar, zai kai mu ga fahimtar cewar sulhun siyasa ne kadai mafi dacewa. Zamu kuma fahimci cewar sai idan an kawo karshn tashin hankali da zub da jini ne, kuma ko wane bangare ya nuna niyyarsa ta samun zaman lafiya da yanci, sa'annan za a sami nasarar kawo karshen halin kaka-ni-kayi da al'ummar Siriya suke ciki. Ga neman sulhun ta hanyar siyasa kuwa, tilas ne gwamnatin tarayya da majalisar dokoki mu hada karfinmu wuri guda."

Har ya zuwa jim kadan kafin a bude taron na Siriya a Montreaux, gwamnati a Berlin tayi fatan kugiyoyin yan tawayen kasar da suka rarrabu zasu sake hade kansu, su halarci wannan taro gaba daya. To amma minista Steinmeier yace yana iya fahimtar mawuyacin halin da kungiyoyin yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi suke ciki, saboda a hannu guda suna yaki da gwamnarin Assad, a daya hannun kuma, suna yaki da kungiyoyi masu matsananin ra'ayi na tarzoma. To amma duk da haka, idan ba tare da kungiyoyin masu sassauicin ra'ayi sun shiga taron ba, zaman lafiyar da ake nema ba zata samu ba. Ministan yace yakin na Siriya, yanzu dai ya zama na nman angizo a wannan yanki, inda ba ma masu ra'ayin Jihadi ne suke cikinsa ba, amma har kasashen Gabas Ta Tsakiya da burinsu shine su raba kan wannan yanki gaba dayansa.

Aussenminister Frank-Walter Steinmeier Porträt
Ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter SteinmeierHoto: Getty Images

Shima mataimakin kakakin yan jam'iyar SPD a majalisar dokoki, Rolf Mützenich ya baiyana damuwa a game da halin da ake ciki a Siriya. Dan siyasar dai ya dade yana lura da halin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya da yankin Gulf. Yace a bayan yakin basasa na shkaru ukku, Siriya tana fuskantar barazanar rushewa ya zuwa ga yankunan kabilu dabam dabam. Jan van Aken, wanda a kwanan nan ne ya komo daga ziyara a arewacin Siriya ya baiyana ra'ayin cewar zaman lafiya ba zai samu ba sai duk wadanda ya kamata a gaiyata a zauren taron dake gudana yanzu sun halarce shi.

"Yace sulhun da ake nema ba zai samu ba sai duk wadanda ya kamata su halarci taron sun hallara. Hakan yana nufin a gaiyaci Iran, a kumagaiyaci Saudi Arabiya, sa'annan daga Siriyan ita kanta duka wadanda suke da hannu a wannan rikici a gaiyace su, ciki kuwa har da Kurdawa. Tushen farko shine a kai ga samun yarjjeniyar tsagaita bude wuta. Ko da ba duka kungiyoyin ne suke halartar taron ba, amma wadanda ake zaune dasu a taburin tattaunawar tilas su amince da yarjejeniyar tsagaita bude wutar, saboda hakan ne kadai zai baiwa al'umar Syria damar sararawa daga wannan tashin hankali."

Syrien Konflikt Bashar Assad Porträt 26. Sept 2013
Jigon rikicin Siriya, shugaban kasa Bashar al-AssadHoto: Reuters

Taron na Siriya an bude shine an kwanaki kalilan bayan da rahotanni suka ce an gano hotuna dake nunar da kisa da azartarwa da gwamnatin Bashar al-Assad ta yiwa dubban yan adawar kasar tun bayan fara yakin shekaru ukku da suka wuce.

Mawallafi: Bettina Marx/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal