1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Kalubalen tsarin iyali a kasashe masu tasowa

Lateefa Mustapha Ja'afar GAT
July 22, 2019

A wannan mako shirin ya duba kalubalan da ke tatatre da tsarin iyali ko saka tazara a tsakanin haihuwa a kasashe masu tasowa irin su Najeriya lmarin da ke illa ga rayuwar uwa da ma danta.

https://p.dw.com/p/3MWA3

A kasashe masu tasowa, akan fuskanci matsala ta yawaitar haihuwa ba tare da la'akari da lafiyar uwa da ma 'ya'yan da takan haifa din ba. Babbar matsalar ita ce rashin aminta da batun tazarar haihuwa tsakanin yaran da ake haifa. 

Shirin na wannan lokaci ya yi nazari ne kan batun tsarin iyali ko kuma bayar da tazarar haihuwa inda ya tattauna da likita da ke zaman masani kan wannan batu da uwa, da kuma malamar addinin da ma kuma al'umma da ta bayyana nata ra'ayin kan wannan batu.