1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya

April 5, 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu ya kaddamar da sabon shirin gwamnati na zaburar da tattalin arzikin kasar cikin wa'adi shekaru Hudu masu zuwa. Hakan dai na zuwa ne kusan shekaru biyu da kama aiki.

https://p.dw.com/p/2alCu
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Tarrayar Najeriyar dai na fatan iya kaiwa ga sarrafa kaso 60 cikin dari na daukacin man da take sha a cikin gida, tare da kaiwa ga wadatar da kai da abinci da sauran bukatu na rayuwa duk dai a tsakanin shekarar bana ya zuwa ta 2020.

Har ila yau dai sabon shirin dake kama da gonar rani na da zummar rage kashe kudade ko dai ga saye na abinci a waje, ko kuma kananan bukatu na rayuwar al'uma; a fadar shugaban kasar da ya kaddamar da shi cikin bikin da ya samu halartar daukacin masu ruwa da tsaki da harkokin mulki a kasar.

"Dole ne mu zamo kasar da zamu iya samar da abun da muke ci da kuma cin abun da muke samarwa. Dole ne mu yi kokarin samar da kudin kasar mu na Naira mai karfi da kuma tattalin arzikinmu mai tasiri. Wannan shirin da nake kadammawa a yau ya fayyace abun da mu a gwamnati muke da burin yi. Mu gina ginshikin da kasuwanci zai bunkasa.  Shirin namu dai na zaman shiri na daukacin kasa"

Matakan kai wa ga nasara

Duk da cewar dai sai a yanzu ne aka yi nasarar kaddamar dashi, tuni dai Abujar ta fara aiwatar da wasu a cikin bangarorin shirin da suka hada da iya kaiwa ga kafa kamfani cikin wattani biyu da kuma saukaka damar shiga kasar a bangare na masu kasuwa. Ko bayan nan dai kuma Abujar da a wannan mako ke shirin sake bude batun dokar masana'antar man fetur, na da tunani na cefanar da kadarorin masana'antar domin mai da su ga masu kasuwa domin tasiri.

Ana dai saran kashe dubban miliyoyi na daloli da nufin kaiwa ga tabbatar shirin da kuma daga dukkan alamu kasar ke da karanci a kai yanzu. To sai dai kuma a fadar Abdul'Aziz Yari Abubakar dake zaman shugaban kungiyar gwamnonin kasar, shirin zai samu goya bayan jihohin dake da burin tallafawa tarrayar domin nasara.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

To sai dai kuma ko bayan matsalar ta kudi, wani abun dake iya zama tarnaki cikin shirin shi ne lokaci ga masu siyasar tarrayar Najeriyar dake shirin sake fuskantar zabe a cikin kasa nan da shekaru biyu. Abin kuma da wasu ke kallon ke iya kai wa ga tsayuwar lamura, dama kila kai karshen nasara ta shirin da kasar ke fatan zai dora ta a kan turbar ci gaba.

To sai dai kuma a fadar Malam Garba Shehu dake zaman kakaki na gwamnatin ta Abuja batun na sake komawa filin daga ba zai yi tasiri a kokari na inganta lamura a kasar ba.

'Yan kasuwa ciki dama wajen kasar dai na fatan shirin zai iya kaiwa ga samar da gamsuwa ta zubin jarinsu dake da muhimmanci ga kaiwa ga samun nasarar da kasar ke hange a gaba