1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ganawar Abbas da Olmert

December 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuX5

Prime ministan Izraela Ehud Olmert da shugaba Mahmoud Abbaas na yankin palasdinawa ,zasu gudanar da wata tattaunawa da aka jima ana jira a ranar 1 ga watan kamawa.Ganawar wadda ke zama na farkon irinsa tsakanin Abbas da Olmert ,ya samu jinkiri adangane na watanni,wanda kuma ake ganin zai jagoranci musayar sojin izraelan dake tsare a yankin,da daruruwan palasdinwa dake jibge a kurkukun Izraelan.Rahotannin jaridun yankin dai na nuni dacewa,shugabannin biyu na shirin ganawa ne gabannin ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice zata kai yankin a kwanakin farkon watan janairu.