1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin gyara dabi'un 'yan Najeriya

Ubale Musa/YBSeptember 8, 2016

A wani abun da ke zaman sabon yunkuri na sauyin lamura cikin kasar da safiyar Alhamis (08.09.2016) shugaban Najeriya ya jagoranci wani sabon kamfen na gyara dabi'un al'ummar kasar.

https://p.dw.com/p/1JyMm
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A cikin raha dama annashuwa ne dai shugaban Tarayyar Najeriyar Muhammadu Buhari ya jagoranci manyan masu ruwa da tsaki a kasar da ma bakinta, wajen kaddamar da sabon kamfen din mai taken "Sauyi ya Fara daga Kaina". Kamfen din kuma da a cikinsa gwamnatin kasar ke fatan sauya dabi'u da ma halayya ta rayuwa da nufin kai wa ga muradun ginin kasar da ke neman subucewa yanzu.

Kama daga sarki ya zuwa talakan cikin kasar dai ra'ayi ya hadu kan cewar fa ta yi baki ta kuma lalace a cikin halayya ta 'yan kasa, abun kuma da a cewar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kai ga rushewar kasar da ma daukar Najeriyar zuwa inda take a yanzu yana mai cewa:

Nigeria Ölrebellen Pipelines
'Yan tawaye a yankin Niger DeltaHoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

"Shi ne dalilin da ya sa wasu ke fasa bututun mai da cibiyoyin mai domin hana kasa samun kudin shiga, shi ne kuma hujjar da ya sa jami'an gwamnati ke sace kudin da aka ba su amana, shi ne kuma damar da wasu ke amfani da ita wajen yin tukin ganganci a tituna, dalili ma ke nan da ya sanya wasu ke sata ta akwatu da ma yin banga yayin zabe, shi ne kuma ya kai tattalin arzikinmu ya fada, yanayi mara kyawun da mu ke neman ceto shi a yanzu".

Abun jira a gani dai na zaman nasara ta shirin da wasu ke kallon da kamar wuya cikin kasar da kowa ya yi imani da rayuwar alfarma.