1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Izra'ila na sakin Falesdinawa

July 28, 2013

Firaministan Izra'ila Benjamin Netanyahu na neman amincewar majalisar ministocinsa dangane da sakin fursunoni 'yan Falesdinu da kasarsa ke tsare da su.

https://p.dw.com/p/19FQ1
Hoto: Reuters

A wannan Lahadin ce Firaministan Izra'ila Benjamin Netanyahu zai nemi amincewar majalisar ministocinsa dangane da shirin nan na sakin Falasdinawa da larabawa 'yan asalin Izra'ila da yanzu haka ake tsare da su a gidajen yarin kasar.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Amirka ke kokarin maida Izra'ila da Falastinu kan teburin sulhu domin warware matsalolin da ke tsakaninsu, sai dai masu aiko da rahotanni na cewar kawo yanzu Izra'ilan ba ta bayyana sunan fursunonin da za a saki ba sai dai ana kyautata zaton wadanda za a saki din na daga jerin wanda aka tsare bisa zargin kashe mata da kananan yara 'yan asalin kasar Izra'ila.

Wannan shirin dai ya sanya iyalan wanda su ka rasu sakamakon rikicin Izra'ila da Falasdinu yin bore domin nuna rashin amincewarsu dangane da sakin fursunonin, yayin da a hannu guda kungiyoyin fararen hula a Falasdinu ke cewar babu wata tattaunawa da za a yi da Izra'ila in har ba a sallami fursunonin ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe