1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kwashe bamabamai masu tarwatsewa a Lebanon.

YAHAYA AHMEDSeptember 1, 2006

A halin yanzu akwai bamabamai masu tarwatsewa kusan dubu ɗari da Isra'ila ta jefa a Lebanon a yaƙinta da ƙungiyar Hizbullahi. Mafi yawan waɗannan bamabaman na nan zube ba su fashe ba. Ko yaya ake tinkarar aikin kau da bamabaman?

https://p.dw.com/p/BtyP
Ɗaya daga cikin ƙauyukan kudancin Libanon da Isra'ila ta ragargaza da bamabamai.
Ɗaya daga cikin ƙauyukan kudancin Libanon da Isra'ila ta ragargaza da bamabamai.Hoto: AP

Tun kusan makwanni 3 ke nan da aka tsagaita buɗe wuta a Lebanon, amma duk da haka, ana ci gaba da samun masu jin raunuka har da ma masu rasa rayukansu, saboda yawan bamabamai masu tarwatsewar da Isra’ila ta jefa, amma waɗanda ba su fashe ba. Bisa ƙiyasin wata cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula yaƙi da nakiyar ƙarƙashin ƙasa, kusan ƙananan bamaban dubu 100 ne ake da su tarwatse a ko’ina yanzu a Lebanon ɗin. Waɗannan kuwa, kafin dai a gano su a kuma kwankwance su, za su kasance wata mugunyar barazana ce ga rayuwar jama’a a yankunan ƙasar. Tuni dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura rukunan ƙwararrun ma’aikata, don su binciko inda bamabaman suke, su kuma kwakwance su. Wata ƙungiyar sa kai ta Birtaniya, wato Mine Advisory Group, na cikin rukunan da ke gudanad da aikin kau da bamabaman a Lebanon. To ko waɗanne irin bamabamai ne masu tarwatsewar? Frank Masche, shugaban tawagar ƙungiyar Mine Advisory Group ɗin, ya bayyana fasalin irin waɗannan bamabaman.

„Wato kamar ƙananan albarusai suke, waɗanda ake haɗa su da yawa cikin wani bututun bam mai kama da roka guda ɗaya. Idan aka harba rokar har ta faɗon inda ake bukata, ta fashe, to sai ƙananan bamabaman su tarwatsu a duk faɗin yankin. Suna iya fashewa su ma, su yi ɓarna, kai tsaye, ko kuma kamar dai a halin da muke ciki yanzu, su ƙi fashewa. To a nan ne fa ake da kasadar. Saboda, idan wani bai sani ba ya taka su, a galibi ya gamu da ajalinsa ke nan.“

Waɗannan ƙananan bamabamn dai ba su da girma. Duk girmansu bai fi na gwamgwanin ruwan lemo ba. Sabili da haka da wuya a gane su, in suna kwance a ƙasa cikin gonaki, ko cikin daji ko ma kan hanyar da mutane ke bi. Wato sai a wayi gari duk fararen hula na huskantar wata mugunyar barazana ke nan. Suna iya ta shi ne kai tsaye da an taɓa su, kamar dai yadda nakiyar ƙaraƙashin ƙasa ke fashewa ko da ɗan yaro ƙarami ne ya ɗora ƙafa a kanta.

To ko yaya ma’aikatan ke kwakwance waɗannan bamabaman kafin su tashi da kansu? Frank Masche ya bayyana cewa, aikin nasu ya dogara ne da yadda kan bam ɗin yake. Idan babu abin da ya taɓa shi, to za a iya ɗaukansa ma aki wani gu daban a fasa shi can. To amma idan aka lura cewa kan ya ɗan karce lokacin da bam ɗin ya faɗo, sai dai fashewa ne bai yi ba, kamata ya yi a lalata shi nan take inda yake. Game da aikin da suuke yi a halin yanzu dai, Masche ya bayyana cewa:-

„Muna bi titi-titi ne, da gidaje da kuma kewayen gidajen da ko’ina dai inda muka san za a sami bam ɗin ko kuma inda mutane suka nuna mana cewa sun ga wani abu mai kama da bam. Yanzu dai, ba mu fara shiga cikin lambuna ko gonaki ko filayen noma ba tukuna. Muna son mu kau da bamabaman daga gidaje da kewayen jama’a ne tukuna, don su iya tafiyad da halin rayuwarsu na yau da kullum ba tare da fargabar tashin wani bam da zai halakad da su ba. Wato aikinmu yanzu dai na taimakon gaggawa ne. Muna zuwa ko’ina inda lamarin ya fi tsanani, mu lalata bamabaman da mutane suka gano kuma suka nuna mana. Burinmu dai shi ne mu taimaki ɗimbin yawan jama’a iya gwargwado“.

Za a dai fara aikin kwashe bamabaman ne sosai, idan ƙungiyoyin ƙwararrun ma’aikatan da dama suka iso Lebanon ɗin da kayayyakin aikinsu. Rukunin Frank Masche dai ba zai iya gudanad da wannan aikin shi kaɗai ba. Da ma can ƙungiyarsa na aikin kau da nakiyar ƙarƙashin ƙasa ne a Lebanon ɗin kafin ɓarkewar yaƙin. To amma yanzu da aka sami wannan sabuwar matsalar, lokacin aikin nasu zai tsawaita.