1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Obama a kan Siriya na samun nasara

Usman ShehuSeptember 5, 2013

Bisa ga dukkan alamu batun kai farmakinm soja kan gwamnatin Siriya, wanda Amirka ke tsarawa ya kama hanya samun izinin 'yan majalisar dokoki

https://p.dw.com/p/19cJX
(L-R) U.S. General Martin Dempsey, chairman of the Joint Chiefs of Staff, U.S. Secretary of Defense Chuck Hagel and U.S. Secretary of State John Kerry testify at a U.S. House Foreign Affairs Committee hearing on Syria on Capitol Hill in Washington, September 4, 2013. The U.S. Senate Foreign Relations Committee struggled on Wednesday to reach agreement on a resolution authorizing military strikes in Syria, but scheduled a vote for later in the day as Obama administration officials pressed for action in Congress. REUTERS/Jason Reed (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Kwamitin da ya amince da kai wa Siriya farmakiHoto: Reuters

Kwamitin harkokin wajen majalisar dattawan Amirka, ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da shirin shugaba Obama na kaiwa ƙasar Siriya farmakin soji, inda aka zargi gwamnatin Siriya da yin amfani da makamai masu guba. Ƙudurin ya amince da yin amfani da soji domin kai farmaki na tsawon kwanaki 90, amma ya haramta tura sojojin Amirka a cikin ƙasar ta Siriya. Shugaba Obama a yanzu haka yana a ƙasashen Turai gabanin taron ƙungiyar ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya da aka sani da G20, inda zai gana da shugabannin ƙasashen China da Japan. Obama dai yana kan yin lallama ce ta samun goyon bayan ƙasashen duniya, bisa manufarsa ta kai farmaki a Siriya, abinda ƙasar Rasha ke matuƙar adawa da shi. Ƙasar China tace farmakin da soja daga ƙasashen waje a kan Siriya, zai yi matuƙar illa ga tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamed Awal Balarabe