1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samar da zaman lafiya a Jos

Mohammad Nasiru Awal
February 19, 2019

A jihar Filato an kaddamar da wani shiri na yafewa juna tsakanin al'ummomin jihar bayan shafe fiye da shekaru 17, da jihar ta  yi fama da tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/3DgXr
Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Hoto: Katrin Gänsler

Kabilun Filato da ke Tarayyar Najeriya daga yankunan kananan hukumomi 17 ne suka hallara waje guda, don yafewa juna irin kura kuran tashe tashen-hankula da suka sami kansu ciki a shekarun baya.

Cibiyar sasantawa da yada kyakkyawar fahimta tsakanin mabiya addinai ta Najueriya wato Interfaith mediation Centre, da ke Kaduna tare da goyon bayan gwamnatin Filato ce ta jagoranci shirin yafiyar, inda shugabanin addinai da shugabanin matasa, sarakunan gargajiya dama shugabanin kabilu daga sassan jihar daban-daban suka hallara a dandali guda tare da kyakyawan kudiri na kawo karshen mummunan yanayi da jihar Filato ta sami kanta shekarun baya.

Jim kadan bayan kaddamar da shirin, gwamnan Filato Simon Lalong, ya ce bayan wannan shiri da aka kaddamar za su fuskanci rikicin manoma da makiyaya, kuma za a rika waiwayawa baya don duba irin nasarori da aka cimma ga wannan shiri na yafiya bayan shekaru biyar.

Daya daga cikin jagororin shirin yafiyar kuma daya a cikin shugabannin cibyiar ta Interfaith Mediation Center, Imam Mohammed Nuraini Ashafa, ya bayyana dalilansu na bullo da wannan salo na yafewa juna tsakanin al'ummar jihar ta Filato.

Yanzu haka dai a cewar Imam Nuraini Ashafa sun kafa wani dandali a tsakyiar birnin Jos da zai zama wurin haduwa don yafe ma juna.

A bangare guda kuma, Pastor James Wuye daya daga cikin shugabannin na cibiyar sasanta mabiya addinai da yada fahimtar juna ta Interfaith, ya ce yanzu kam an dauki kyakkyawar alkibla ta kawo zaman lafiya mai dorewa a Filato ganin yadda aka fara da yafewa juna.

Josepf Lemang shi ne shugaban ma'aikatar wanzar da zaman lafiya da sulhu a jihar Filato ya yi karin haske yadda kungiyar Interfaith da gwamnati da ma sauran kungiyoyi masu zaman kansu ke ba da gudunmawar ganin an zauna lafiya da juna tsakanin kabilu da mabiya addinai dabam dabam a Filato.

Dandali Chiroma shugaban makiyaya na arewa ta tsakiya daya a cikin shugabannin al'umma da ke hada kai da sauran kungiyoyin yankin da ma hukumomi don wanzar da zaman lafiya, ya nuna farin cikinsa da wannan ci-gaba da aka samu a kokarin shimfida turba ta yafiya tsakanin al'ummar jihar Filato.

Su ma matasan jihar sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan shiri na yafiya suna masu dangana shi da yanayin siyasar kasar.

Al'ummar Filato da dama sun bayyana goyon bayansu tare da fatan cewar wannan kudiri zai zama wata hanyar da za ta samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar ta Filato.