1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tsayar da ranar zaɓe a Poland

April 13, 2010

Muƙaddashin shugaba Poland ya ce gobe laraba zai baiyana ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

https://p.dw.com/p/MvRO
Hoto: dpa-Bildfunk

Muƙaddashin Shugaban ƙasar Poland, wato Bronislav Komorowski ya fara tattauna da ɓangarori daban daban na ƙasar domin tsayar da ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa. Cikin wani jawabi da yayi a tashar talabijin ɗin ƙasar, Komorowski ya ce gobe laraba ne idan Allah ya kaimu zai sanar ma yan ƙasar tartibiyar ranar da za su kaɗa kuri´arsu domin zaɓen wanda zai gaji Lech Kazinski.

Bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasar ta Poland, kan nan kwana da 4 ga watan yuli ne ya kamata a zaɓin shugaban da zai maye gurbin mariyayin.

Majalisun dokoki da kuma na tarayya na ƙasar ta Poland sun fara wata zama ta musamman domin karrama shugaba Lech Kazinski da ya rasa ransa a wani haɗari na jirgin sama a ƙasar Rasha. Ranar asabar ko kuma lahadi ne ake sa ran gudanar da jana´izar shugaban na Poland da kuma mai ɗakinsa.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita:Zainab Mohammed Abubakar