1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tura sojojin KTT zuwa kasar Kongo

May 15, 2006

A yau ne ministocin tsaro na kasashen KTT ke taronsu a Brussel domin nazarin shirin tura sojojinsu zuwa Kongo

https://p.dw.com/p/Bu06
Sojan MDD a Kongo
Sojan MDD a KongoHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Rahotanni masu nasaba da wata jarida a nan Jamus sun ce ministan tsaron kan kasar Franz Josef Jung yayi kakkausan suka akan yadda ake tafiyar da shirye-shiryen tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na kasashen Turai zuwa janhuriyar demokradiyyar Kongo, domin kuwa kawo yanzu ba’a tantance yadda za a raba nauyin matakin daidai-wa-daida tsakanin illahirin kasashen kungiyar ba. Fritjof Schmidt wakilin jam’iyyar the Greens a majalisar dokoki, wanda ke adawa da manufar tura sojojin ya ce shirye-shiryen na fama da gibi da kuma tafiyar hawainiya. A ganinsa MDD, wadda tun shekarun da suka wuce take da sojojinta a kasar Kongo, ita ce nauyin tafiyar da al’amuran tsaron ya rataya a wuyanta. Schmidt ya kara da cewar:

1.O-Ton Schmidt

Abin takaici ne kasancewar sau biyu kwamitin sulhu na MDD na hana ruwa gudu game da kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya a Kongo MONUC a takaice. A saboda haka aka billo da wannan sabon salo na neman taimako, saboda har yau kwamitin sulhun ya ki amincewa da kara yawan sojojin daga dubu 17 zuwa dubu 20, kuma ba wanda ya san dalilin haka. Lamarin baki dayansa na tattare da walakin.

Akwai dai bukatar gabatar da wani mataki na gaggawa domin shawo kan wannan matsala, domin kuwa zaben na kasar Kongo, wanda shi ne na farko da zai gudana a demokradiyyance, za a tafiyar da shi ne a ranar 30 ga watan yuli mai zuwa. An shirya Kungiyar tarayyar Turai zata ba da gudummawar sojojin 1500 domin sa ido akan zaben da kuma rufa wa sojojin kiyaye zaman lafiya na MONUC baya. Ana bukatar dakarun soja dari biyar daga Jamus. Babban abin da ake fatan tantancewa a wannan makon shi ne maganar kudi da yawan sojojin da kowace kasa ta kungiyar zata bayar da kuma ta hakikanin alkiblar da za a fuskanta dangane da wannan mataki, wanda zai shafi fadar mulki ta Kinshasa ne kawai. Masu sukan lamirin manufar sun ce wajibi ne a fayyace wa sojojin na KTT ainifin alhakin da ya rataya a wuyansu. Domin kuwa tura sojojin zuwa kasar ta Kongo dake fama da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa abu ne dake tattare da kasada. A karshen makon nan da ya wuce mai sai da wasu dakarun ‘yan tawaye suka kai farmaki kan wani sansani na soja, inda aka halaka mutane 50. Har yau da sauran rina ab kaba dangane da zaman lafiyar Kongo, inda da yawa daga sojojin sa kai ke kyamar duk wata manufa ta warware rikicin a cikin lumana. A saboda haka ya zama wajibi a yi wa shirin na tura sojojin Kungiyar ta Tarayyar turai wani takamaiman tsari bisa manufa.