1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ziyarar Shugaban China a Saudiyya, Iran da Masar

Sailissou BoukariJanuary 15, 2016

Bayan da wani jami'in diflomasiyyar kasar China ya yi kira ga kasashen Saudiyya da Iran da su zuba wa zukatansu ruwa, Shugaba Xi Jinping ya shirya wata ziyara zuwa kasashen.

https://p.dw.com/p/1HeGZ
Hoto: Reuters/L. Hongguang/Xinhua

Ministan harkokin wajan kasar ta China Lu Kang ne ya sanar da wannan labari ta shafin ofishinsa na Internet, inda ya ce wannan ziyara za ta fara daga ranar 19 ga zuwa 23 ga wannan wata na Janairu. Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da wani jami'in diflomasiyyar kasar ta Sin ya yi kira ga kasashen Saudiyya da Iran da su zubawa zukatansu ruwan sanyi domin mutunta dangantakar da ke tsakaninsu, wadda ta riga ta yi tsami tun bayan aiwatar da hukuncin kisa da Saudiyya ta yi ga wani shehin malami dan Shi'a Nimr Al-Nimr, wanda hakan ya janyo fushin kasat ta Iran.