1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen bikin cikar Mandela shekaru 95 a duniya

July 17, 2013

A bana tsohon dan gwagwarmayar kwatar 'yancin bakar fatar Afirka ta Kudu kuma tsohon shugaban kasar zai yi bikin ranar haihuwarsa a asibiti, inda ake yi masa jiyya.

https://p.dw.com/p/199hH
Former South Africa's President Nelson Mandela is pictured during an interview with the media at is house in Qunu, South Africa,18 July 2008. Mandela, the anti-apartheid icon spend his 90th birthday at home in Qunu with his family, and the whole village is celebrating EPA/THEMBA HADEBE
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da a ranar Alhamis tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela zai yi bikin cikarsa shekaru 95 da haihuwa a kan gadon asibiti inda ake masa magani, duniya na ci gaba da yi masa fatan alheri tare da gudanar da ayyuka na gari. A Afirka ta Kudu kungiyoyin masu hawa keke za su yi aikin gayya na share tituna sannan masu aikin sa kai za su yi fentin makarantu yayin da su kuma a nasu bangare 'yan siyasa za su sadaukar da mintoci 67 don gudanar da muhimman ayyukan agaji don girmama shekaru 67 da Mandela yayi yana yi wa jama'a aiki. A shekarar 2010 Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar haihuwar Mandela, wanda ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel, a matsayin ranar Mandela, amma ga da yawa bikin na bana na da matukar muhimmanci. Mandela dai ya shafe makonni shida da suka gabata a wani asibitin birnin Pretoria inda har yanzu yake fama da matsanancin rashin lafiya ko da yake an ce babu abin fargaba a ciki.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu