1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zabe a gabashin Jamus

Abdul-raheem Hassan
September 11, 2017

Wakilan sashen Afirka da suka hada da sashen Hausa da Ingilishi da Faransanci da Amharic da kuma Suwahili sun fara rangadi na musamman a wasu garuruwa da ke Gabashin Jamus da kan iyakar Jamus da Poland.

https://p.dw.com/p/2jjEQ
DW Pan-Africa “Germany Decides”
Ma'aikatan sashen Afirka na DW dake rangadi a Gabashin JamusHoto: DW/U. Shehu

Wannan rangadi dai zai maida hankali ne kan yadda mazauna yankunan ke shirye-shiryen shiga zabukan gama-gari da za a gudanar a ranar 24 ga watan Satumba na shekara ta 2017. 

Cikin muhimman abin da wakilan harsunan Afirka na DW za su maida hankali a yayin ziyarar sun hada da tasirin jam'iyun da ke takara ganin yadda ake samun 'yan Afirka da dama da suka yi karatu a wasu garuruwa da ke gabashin kasar musamman garin Leipzig.

Kuna iya rubuto mana dukkanin tambayoyinku kan abin da ku ke son sani a kan zaben na Jamus dama tsarin siyasar kasar a shafinmu na sada zumunta na Facebook.