1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya fara ziyarar yankin Gabsa ta Tsakiya.

January 9, 2008
https://p.dw.com/p/CmoS

Shugaban Amirka Geroge Bush ya na kann hanyarsa zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda zai fara yada zango a Izraila da Gabar Yanma, da niyar taimakawa wajen sake zama kann teburin shawara domin ci gaba da neman bakin zaren war-ware rikicin yankin, bayan an sake tayar da tattaunawa kann cimma zaman lafiya na yankin a birnin Annapolis. Kafin ya bar Amirka, Bush ya yi jawabi ga manema labarai inda ya bayyana fatar cewar za’a cimma yarjejeniya mai ma’ana kafin karshen wannan shekara. Bayan ya tattauna da shugabannin Izraila da na Palestinawa, Bush, zai ci gaba da ziyararsa na mako daya, a sauran kasashen larabawa biyar dake hulda da Amirka. A ƙarshe shugaba Bush ya shaidawa kafofin yaɗa labarai cewar zai yi amfani da wannan ziyarar wajen tunawa ƙasashen larabawa cewar nauyin tabbatar da an kafa wadannan kasashen biyu ya rataya a garesu.