1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya sanya hannu kan sabuwar dokar yaki da ta'addanci

October 17, 2006
https://p.dw.com/p/BufW

Shugaban kasar Amurka George Bush ya sanya hannu akan dokar nan ta yaki da taaddanci,wadda ta bada damar daukar tsauraran mataki wajen tambayoyi ga wadanda ake zargi da alifin taaddanci.

Dokar wadda ake rigima akanta ta akuma baiwa gwamnati damar gurfanar da wadanda ake zargin gaban hukumomin soji.

Bush yace dokar zata taimaka kare tsaron kasar.

Wannan doka ta fara aiki ne makonni shida bayan Bush ya amince cewa CIA tana da wuraren yiwa wadanda take zargi tambayoyi a kasashen ketare .

Shugaban na Amurka tunda farko ya bukaci majalisar dokokin kasar data gaggauta amincewa da dokar bayanda kotun koli ta kasar tayi watsi da shi.