1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Donald Trumps na ziyara a kasar Faransa

Salissou Boukari
July 13, 2017

Da safiyar wannan Ahamis din ce shugaban Amirka Donald Trump ya sauka a birnin Paris na kasar Faransa, a wata ziyara da zai yi ta kwanaki uku a kasar, inda zai gana da Shugaban na Faransa Emmanuel Macron.

https://p.dw.com/p/2gUEx
Frankreich Donald Trump im Elysee Palace
Shugaban Amirka Donald Trump da na Faransa Emmanuel Macron yayin taron manema Labarai a birnin Paris.Hoto: Reuters/G. Fuentes

Da yammacin ranar Alhamis ce Shugaban Amirka Donald Trump da ke ziyara a kasar Faransa ya jagorancin taron manema labarai tare da takwaransa na kasar ta Faransa Emmanuel Macron. Yayin taron shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi hulda tsakanin kasashen biyu, da kuma matakan dauka a nan gaba kan batutuwa da dama. kaman yadda Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyanasu: 

"Ina iya cewa bisa manyan batutuwa da muka tattauna kaman na harkar kasuwanci, da batun tsaron kasashenmu, da yaki da ta'addanci da kuma neman zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, da ma kasar Libiya da yankin Sahel dukanninmu muna da buri guda kan wadan nan fannoni."

Shugaban kasar ta Faransa ya ce yana mai cike da biyayya ga mataki shugaba Trump kan yarjejeniya yaki da dumamar yanayi ta birnin Paris, inda ya ce duk da haka za su ci gaba da tattaunawa dan ganin an samu sassauci a mataki da shugaba Trump ya dauka. Daga nashi bangare shugaban Amirka Donald Trump ya yaba kamun luddayin shugaban na Faransa, inda ya ce mutun jarimi wanda zai iya tafiyar da jagorancin wannan kasa ta Faransa. Shugaban na Amirka zai halarci fareitin sojoji kasar ta Faransa a ranar Juma'a 14 ga watan Yuli.