1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Jacob Zuma na shirin jawabinsa na shekara-shekara

Salissou Boukari
February 9, 2017

Da yammacin wannan Alhamis Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, zai gabatar da jawabinsa na shekara-shekara a gaban majalisar dokokin kasar da ke birnin Cape Town cikin kwararan matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/2XCr2
Afrika Jacob Zuma
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Hisham

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Laraba, ta ce ta dalilin halin da ake ciki na bore daga bangaren 'yan adawar kasar, gwamnati ta dauki aniyar karfafa matakan tsaro a kewayen majalisa, inda ta kira karin sojoji 400 domin ban hannu ga sauran jami'an tsaro yayin jawabin na Shugaba Jacob Zuma.

Sai dai tuni babbar jam'iyyar adawa ta "Democratic Party" ta mayar da martani kan wannan sanarwa, inda ta ce ba za ta zura idanu tana kallon a mayar da majalisa a matsayin wani fili na nuna karfin soja don kawai a basu tsoro ba. Daga nata bangare jam'iyyar EFF danganta matakin ta yi da ayyana yaki ga 'yan kasa.

Tun dai yau da shekaru biyu da suka gabata, jawabin shekara-shekara na shugaban kasar ta Afirka ta Kudu ke fuskantar tashe-tashen hankula daga 'yan adawa da suka sha neman a kawar da shi daga kan karagar mulkin kasar ba tare da cin nasara ba.