1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Khadafi ya shawarci girka gwamnatin haɗin kan Afrika

July 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuHH

Saban shugaban ƙungiyar gamayya turai, bugu da ƙari Praministan Portugal, Jose Socrates, ya gabatar da wani mahimmin jawabi, a taron ƙoli karo na 9, na ƙungiyar taraya Afrika, da aka rufe yau a birnin Accra na ƙasar Ghana.

Socrates ya alƙawarta gudanar da kwaskawarima ga mu´amila tsakanin Afrika da ƙasashen turai.

Za shi bayyana mayan matakan da kwaskwarimar ta tanada a taron da zai haɗa ɓangarorin 2, a birnin Lisbonne, na Portugal daga 8 zuwa 9 ga watan desember.

Saidai tunni, ya ce batutuwan kare haƙƙoƙin bani adama, yaƙi da talauci, da kuma kwararar baƙin haure, za su kasance ƙashin bayan sabuwar mu´amila tsakanin Afrika da EU.

A jawabin da yayi albarkacin rufe wannan taro, shugaban ƙasar Lybia, Muhhamad Khaddafi, ya bada shawara girka haɗɗaɗiyar gwamnatin nahiyar Afrika, ranar 1 ga wata Janairu na shekara ta 2008.

Wannan gwamnati zata ƙunshi ministoci 15, da su ka haɗa da ministan tsaro , da na harakokin waje, da kuma ministan kasuwanci da ƙasashen ƙetare.

Shugaba Khaddafi, ya bukaci ƙungiyar AU,ta girka komitin shugabanin ƙasashe 5, wanda za su ci gaba da tunani a game da yiwuwar kafa gwamnatin Afrika.