1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Lula da Silva ya lashe zaɓen ƙasar Brazil

YAHAYA AHMEDOctober 30, 2006

’Yan ƙasar Barzil kusan miliyan ɗari da 25 ne suka ka da ƙuri’u a zagaye na biyu, don zaɓan shugaban ƙasa. ’Yan takara a zaɓen dai su ne shugaba mai ci yanzu Lula da Silva na jam’iyyar PT ta ma’aikata da abokin hamayyarsa Geraldo Alckmin na jam’iyyar Social Democrats. Sakamakon zaɓen dai na nuna cewa, shugaba Lula ne ya sami rinjayi da kashi 60 da ɗigo 8 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da, yayin da Geraldo Alckmin, ya sami kashi 38 da digo 2 cikin ɗari. Wannan sakamakon dai na nuna cewa ’yan ƙasar Brazil sun amince da wa’adi na biyu ke nan na shugaba Lula.

https://p.dw.com/p/BtxZ
Shugaba Lula da Silva na ƙasar Brazil a yaƙin neman zaɓe.
Shugaba Lula da Silva na ƙasar Brazil a yaƙin neman zaɓe.Hoto: AP

A lokacin wa’adin aikinsa na farko dai, shugaba Lula da Silva na Ƙasar Brazil ya sha fama da taɓargaza iri-iri. Sabili da haka ne kuwa, masharhanta da dama suka yi ta mamakin yadda ya iya lashe wannan zaɓen da babban rinjayi.

Amma idan aka dubi lamarrin ta huskar ’yan ƙasar Brazil ɗin, za a ga cewa, a wurinsu, kusan duk ’yan siyasa da jam’iyyun ƙasar, na da hannu a wata taɓrgaza ta cin hanci da rashawa. Sabili da haka ne wannan batun bai dame su ba. Abin da ya fi damunsu shi ne, daga cikin ’yan takaran, wanne ne zai fi kula da ɗaukan matakan inganta halin rayuwarsu?

Ita dai jam’iyyar PT ta ma’aikata da shugaba Lulan da kansa sun cim ma nasarar janyo hankullan mafi yawan ƙasar su goyi bayan manufofin da suka gabatar musu, tare kuma da nanata musu irin nasarorin da gwamnatin shugaban ta samu a wa’adin aikinta na farko. Ɗaya daga cikin manufofin da gwamnatin shugaba Lulan ta aiwatar dai, ita ce manufar nan ta inganta halin rayuwar talakawan ƙasar da ya gabatar, wadda aka fi sani da suna Bolsa Familia. A yankin arewa maso gabashin ƙasar ne kuwa, iyalai da yawa, masu ƙananan albashi da marasa abin biyan bukatunsu na yau da kullum, suka fi cin moriyar wannan shirin.

Ba abin mamaki ba ne kuwa, da kashi 77 cikin ɗari na al’umman wannan yankin suka ka da wa shugaba Lula ƙuri’unsu. A yankunan da aka sansu ma da bin ra’ayin ’yan mazan jiya, kamarsu jihar Bahia, shugaba Lulan ne ya fi samun rinjayi. Ta hakan ne kuwa, ya iya cike giɓin asarar ƙuri’un da ya yi a kudancin ƙasar.

Masu sa ido a zaɓen dai sun ce, tsarin gudanad da camfen da shugaba Lulan ya bi ma, ya ƙara taimaka masa wajen lashe zaɓen. A zagaye na farko dai, shugaban ya guji yin muhawara da abokan hamayyarsa a kan talabijin, abin da ɓangarori da dama ke gani kamar babban kuskure ne. A lokacin yaƙin neman zaɓe a zagaye na biyun kuwa, shugaban bai yi wata wata ba, wajen huskantar abokin hamayyarsa Geraldo Alckmin, a duk wata muhawarar da aka yi a bainar jama’a da kuma kan talabijin. Bugui da ƙari kuma, a wannan karon, ba a sami wata taɓargaza a jam’iyyar ta PT ba, wadda za ta iya shafa wa sunansa kashin kaza.

A daura da shugaba Lula kuwa, shi Geraldo Alckmin, wanda ya tsaya tamkar ɗan takarar jam’iyyun PSDB da PFL, masu bin ra’ayin ’yan mazan jiya, bai iya ya janyo hankullan jama’a da dama wajen amincewa da goyon bayan shirinsa ba. A huskar tattalin arziki, bai iya ya gamsad da mutane da manufofinsa kamar yadda shugaba Lula ya yi ba. Tsarin da ya gabatar na ƙara zuba jari a harkokin tattalin arzikin ƙasar da rage haraji, bai gamsad da al’umman Brazil ɗin ba, waɗanda ke ganin aiwatad da shirin ba abu ne mai yiwuwa ba.

Alckmin dai ya yi ƙoƙarin mai da batun gurɓacewar yanayi da yawan sare ƙundurman dazuzzukan Brazil ɗin ne tamkar muhimman jigoginsa. Amma hakan bai janyo masa goyon bayan da ya yi fatar samu ba.

Zaɓen na ƙasar Brazil dai, ya kasance ne cikin wani yanayi inda masu ka da ƙuri’un suka iya tsai da shawara kan wanda suke son ya mulke su, daga cikin ’yan takaran guda biyu. Duk da cewa shi ma shugaba Lulan taɓargaza ta shafe shi, amma mafi yawan ’yan ƙasar musamman talakawa da masu ƙaramin albashi, sun zaɓe shi ne saboda kyakyawan shirin da ya gabatar, kuma yake aiwatarwa na tabbatar wa talakawan samun albashi, wanda komin ƙanƙancinsa dai, zai ishe su biyan bukatunsu na yau da kullum.