1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Turkiya sun hada kai kan 'yan gudun hijira

Yusuf Bala October 18, 2015

Yayin da EU ta sa himma a shawo kan matsalar kwarar 'yan gudun hijira zuwa Turai ita kuwa Turkiya ta ce lugudan wutar da ake yanzu a Siriya zai kara yawan 'yan gudun hijirar.

https://p.dw.com/p/1Gq5G
Pressekonferenz Merkel Davutoglu
Shugaba Merkel da Firayim Minista Ahmet DavutugluHoto: Reuters/M. Sezer

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Lahadin nan ta tattauna da shugabanni a ƙasar Turkiya inda ta sake jaddada buƙatar ƙasashen na Turai wajen ba da tallafi ga ƙasar yayin da ita kuma za ta yi ƙoƙari ta hana 'yan gudun hijira masu ratsa iyakar kasarta zuwa kasashen na Turai.Shugabar dai ta tattauna da Firaminista Ahmet Davutuglu da shugaba Recep Tayyip Erdogan yayin da wannan ziyara da ke zuwa a daidai lokacin da ake samun sabbin dubban 'yan gudun hijira da bakin haure na zuwa kasashen.

Cikin abin da Ƙungiyar ta EU dai ta ƙudiri aniyar ba wa ƙasar ta Turkiya sun hadar da tallafi da zai kai Euro miliyan dubu uku dan ƙasar ta dafawa ayyukanta na jinkai ga 'yan gudun hijira sama da miliyan biyu da ke a ƙasarta, baya ga saukaka batun samun "Visa" ga 'yan ƙasar ta Turkiya zuwa Turai sannan a sake nazari kan batun buƙatar ƙasar ta zama mamba a kungiyar ta EU.