1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Obama da Castro sun yi musabaha

Yusuf BalaApril 11, 2015

A cewar sakataren janar na MDD Ban Ki-Moon bayyanar ta shugaba Raul Castro a wajen taron wani abu ne da aka dade ana jimirin gani. Bisa fatan sauyi a kasar mai bin tsarin kwaminisanci

https://p.dw.com/p/1F6Ei
Obama und Castro in Panama
Hoto: picture-alliance/dpa

A cewar Bernadette Meehan da ke magana da yawun cibiyar samar da tsaro a Amirka, shugabannin biyu sun hadu suka gaisa kafin bude taron kolin na kasashen Latin Amirka da ke gunadana a Panama .

Shugaban kasar ta Cuba Raul Castro da shugaba Barack Obama na Amirka, sun yi musabahar ne a jiya Juma'a karon farko da shugabannin kasashen biyu ke ganawa, tun bayan da aka shiga tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu a farkon shekarar 1961.

Wannan gayyata da aka yi wa kasar ta Cuba dai, na zama karon farko da aka yi mata dan halartar taron kasashen Latin na Amirka.

A cewar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, bayyanar ta shugaba Raul Castro a wajen taron wani abu ne da aka dade ana jimirin gani.

Shugaba Castro kafin ya zauna cikin jerin shugabanni a wajen taron, ya tafa da ma dan yin wasannin ban dariya da shugaba Juan Carlos na kasar ta Panama da mai dakinsa.