1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka ta Kudu ya lashe zaben jam'iyyar ANC

December 18, 2012

Jam'iyyar ANC mai mulki kasar Afirka ta Kudu ta zabi Shugaba Jacob Zuma domin ci gaba da rike shugabancin jam'iyyar

https://p.dw.com/p/1750z
Hoto: picture-alliance/dpa

Jam'iyyar ANC mai mulki kasar Afirka ta Kudu ta zabi Shugaba Jacob Zuma domin ci gaba da rike shugabancin jam'iyyar, yayin da hanshakin dan kasuwa Cyril Ramaphosa ya lashe zaben mataimakin shugaban jam'iyyar.

Wannan yayin da wakilai kusan 5000 ke cigaba da gudanar da babban taron jam'iyyar ta ANC, kuma mataimakin shugaban kasar Kgalema Motlanthe, ya kalubalanci shugaba Zuma a takaran.

Haka ya tabbatar da cewa Zuma zai cigaba da shugaban kasar ke nan inda zai samu dama ta biyu, idan wannan wa'adin ya kare.

Cikin shekara ta 2009 aka zabi Jacob Zuma a karon farko na wa'adin mulkin shekaru biyar na kasar ta Afirka ta Kudu. Kuma cikin shekara ta 2014 za sake gudanar da zaben kasa baki daya, lokacin da ake saran Shugaba Zuma dan shekaru 70 da haihuwa, zai samu wa'adi na biyun.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman