1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa na ziyara a Bangui

February 28, 2014

Shugaba Francois Hollande ya tabbatar da shirin kasar na ganin samun zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1BHVz
Hoto: Getty Images/Afp/Sia Kambou

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta gargadin cewa rikicin da yake faruwa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya yi kama da kisan kare dangin da ya faru a Bosniya cikin shekarar 1995.

Babban jami'in hukumar mai kare fararen hula Philippe Leclerc wanda ya dawo daga kasar bayan kwashe watanni biyu, ya ce Musulman kasar suna fuskantar yanayi da ya yi kama da abun da Musulman Bosniya-Hercegoviva suka fuskanta cikin shekarun 1990, kuma abun da ke zama lamari mafi muni da nahiyar Turai ta fuskanta tun bayan yakin Duniya na biyu.

A wannan Jumma'a Shugaban Faransa Francois Hollande ya isa birnin Bangui fadar gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda dakarun kasar da sauran na kasashen Afirka ke aikin neman tabbatar da doka da oda. Yayin ziyarar Hollande ya gana da shugabar gwamnarin rikon kwarya Catherine Samba Panza da kuma dakarun da ke aikin kiyaye zaman lafiya, inda ya ce kasarsa ta tura daruruwa dakaru domin kare Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daga daidaicewa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe