1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea: Alpha Condé zai yi tazarce

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
September 1, 2020

Jam'iyyar da ke mulki a Guinea Conakry ta sanar da tsayar da Shugaba Alpha Condé a matsayin dan takararta, inda zai nemi wa'adi na uku a zaben da zai gudana a ranar 18 ga watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/3hrSQ
Guinea Präsident Alpha Condé
Shugba Alpha Condé na kasar GuineaHoto: Getty Images/C. Binani

Idan za a iya tunawa dai, mutane da dama ne suka mutu a kasar Guinea Conakry, sakamakon rikicin da ya biyo bayan yunkurin Conde na kwaskware kundin tsarin mulkin kasar domin samun damar yin tazarce. Tun a farkon watan Agusta ne jam'iyyar RPG da ke rike da mulkin Guinea ta nemi shugaba Alpha Condé ya sake tsayawa takara karkashin inuwarta, amma ya gindaya mata sharadin tsara manufofi da za su kawo wa mata da matasa ci gaba mai ma'ana a kasar. Faransa ta yi watsi da zaben Guinea Wannan ne ya sa jam'iyyar ta shata wani daftari na ayyukan raya kasa da Alpha Condé ya amince da shi, bayan da ta bayyana hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da su.

Me kundin tsarin mulki ya tanada?

Sai dai sabanin wa'adinsa na farko da na biyu, inda ya Shugaba Condé da kansa ya bayyana takararsa, a wannan karon jam'iyyarsa ta RPG ce ta fitar da sanarwar da aka karanta a gidan talabijin mallakar gwamnati.Kundin tsarin mulkin Guinea ya takaita yawan wa'adin shugabancin kasa zuwa biyu, amma magoya bayan Condé sun yi ikirarin cewa sabon kundin tsarin mulkin da aka samar karkashin zaben raba gardama da 'yan adawa ba su halarta ba, ya ba shi damar neman sabon wa'adi na mulki.

Guinea Wahlkampf 2015
Gangamin yakin neman zaben Conde a 2015Hoto: DW/B. Barry

Kakakin jam'iyya mai mulki RPG Domani Doré ya ce, shugaban na Guinea ya yi amfani da wannan dama wajen harbin tsuntsu biyu ne da dutse daya: "Farfesa Alpha Condé ya yi muhimman abubuwa biyu a karkashin wannan takara da ya karba: Na farko, ya jadadda abin da ya saba fada ko yaushe cewa zai yi abin da mutane suka ce ya yi. Wannan ita ce hujjar cewa yana mutunta abin da jama'a da jam'iyyarsa ke so, kuma ya girmama jam'iyyar da ke goyon bayan takararsa. Dole ne mu mutunta tushen dimukuradiyya. Tabbas, doka ta ba shi damar ya tsaya takara bayan zaben raba gardama, kan kwaskare kundin tsarin mulki."

Wa'adi na uku: Sabon salon kama karya

Sai dai gamayyar FNDC ta jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da na kwadogo, sun yi amfani da kakkausan lafazi wajen yin tir da neman tazarcen da Shugaba Condé ya yi, inda ta ce ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar da ya kayyade wa'adi biyu kacal. Tazarcen Alpha Conde na samun cikas A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta bayyana yunkurin tazarce na Condé a matsayin "kama-karya," inda ta nuna cewa a Larabar wannan makon za ta rubanya zanga-zangar da ta shafe tsawon watanni tana gudanarwa, zanga-zangar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa.

Guinea Conakry  | Proteste gegen Tötung von Demonstranten und gegen Präsident Alpha Conde
Zanga-zangar adawa da Alpha CondeHoto: Getty Images/AFP/C. Binani

Tun a watan Oktobar shekara ta 2019 ne dai, gamayyar FNDC take fafutukar ganin Alpha Condé ya nemi wa'adin mulki a karo na uku ba tare da hakarta ta cimma ruwa ba. Bah Oury, shugaban jam'iyyar adawa ta UDRG ya ce dama ya san shugaba Condé zai rina, wato zai sake tsayawa takara: "Wannan ba  abin mamaki ba ne, saboda tun da dadewa Alpha Condé ya bayyana cewa jam'iyyarsa ce za ta yanke shawara kan takarar wa'adi na uku, kuma abin da ya faru ke nan a karkashin sanarwar da ta fitar. Wannan wata dabara ce ta karkartar da hankulan wasu mutane su yi tunanin cewa Condé bai yi nufin sake tsaya wa takara ba, bayan haka kuma ya dagulawa 'yan siyasa lissafi. A takaice dai, wata dabara ce ta cin lokaci, domin samun sukunin shirya hanyar bayyana takararsa."

Zanga-Zangar adawa a Guinea Alpha Condé mai shekaru 82 a duniya, wanda kuma ya dade yana adawa kafin ya dare kan kujerar mulki a shekara ta 2010, ya zama shugaba na farko da aka zaba ta hanyar dimukuradiyya a kasar ta Guinea Conakry. Sai dai a wannan kasa ta yammacin Afirka da Faransa ta mulka, fiye da rabin al'ummarta na rayuwa cikin talauci duk da arzikin karkashin kasa da Allah ya hore mata. Ko da lokacin da aka sake zabarsa a shekara ta 2015, sai da abokan hamayyar Alpha Condé suka zarge shi da rashin tabuka wani abun a gani a yaba ga kasar.