1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Hisbollah ya ce ana tattaunawa da Isra´ila

November 1, 2006
https://p.dw.com/p/Budk
Shugaban Hisbollah Sayyed Hassan Nasrallah ya ce an fara wata tattaunawa tsakanin kungiyarsa da Isra´ila ta hanyar wani mai shiga tsakani na MDD don yin musayar firsinoni. A lokacin da yake magana ta tashar telebijin din kungiyar Hisbollah Nasrallah ya ce ana gudanar da wata tattaunawa ta gaske da wani wakilin MDD da bai bayanna sunansa ba. A ranar 12 ga watan yuli Hisbollah ta yi garkuwa da sojojin Isra´ila biyu a wani hari da suka kai kan iyaka. Hakan ya haddasa yakin kwanaki 34 da aka gwabza tsakaninta da rundunar Isra´ila a kudancin Libanon. Kawo yanzu Isra´ila ba ta ce uffan ba game da kalaman na Nasrallah.