1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da girke sojojin Jamus a kasar Jordan

Zulaiha Abubakar MNA
January 29, 2018

Steinmeier ya yi wannan furuci ne bayan ganawarsa da sojojin kasar 300 a wani sansanin sojin sama a arewa maso gabashin Jordan.

https://p.dw.com/p/2rjNE
Libanon- und Jordanien-Reise des Bundespräsidenten
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Carstensen

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewar mayar da dakarun Jamus kasar Jordan daga kasar Turkiyya a cigaba da kokarin magance ayyukan 'yan kungiyar ta'addanci ta IS wani abin a yaba ne.

Steinmeier ya yi wannan furuci ne bayan ganawarsa da sojojin kasar 300 a wani sansanin sojin sama a arewa maso gabashin kasar Jordan. Ya kuma kara da cewar ya zuwa yanzu yaki da ta'addanci ya samu nasara, don haka ana dada bukatar sojojin domin su hana wadanda suka yi ragowa daga cikin 'yan ta'addan cigaba da tasiri.

 

Tun da fari sai da ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira na Azraq, gurin da a halin yanzu ya zama matsugunin kimanin 'yan gudun hijira dubu 36 daga kasar Siriya. Ita dai kasar Jordan ta garkame iyakokinta da kasar Siriya tun a shekara ta 2016 yayin da aka kai wani mummunan harin bam da wata mota.