1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kasar Jamus A Shelkwatar AU

December 15, 2004

A yau laraba ne shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya gabatar da jawabi ga babbar mashawartar Kungiyar Tarayyar Afurka (AU) a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha

https://p.dw.com/p/BveB
Shugaban Kasar Jamus Horst Köhler
Shugaban Kasar Jamus Horst KöhlerHoto: AP

An samu kyawawan canje-canje masu ma’ana ga al’amuran Afurka in ji shugaban kasar Jamus Horst Köhler a lokacin da yake bayanin sakamakon ziyararsa ta kwanaki goma ga kasashen Afurka. A cikin jawabin da ya gabatar a babbar mashawartar Kungiyar Tarayyar Afurka dake Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha Köhler ya sake nanata kira a game da dora dangantakar kasashen Afurka da kasashe masu ci gaban masana’antu akan wata sibga ta adalci da zata amfanar da dukkan bangarorin biyu. Ya ce Afurka na taka muhimmiyar rawa a huldodin dangantaku na kasa da kasa kuma tana da al‘adunta. Amma fa sai ya kara da cewar:

Amma fa har aba da ba zan taba yarda da yadda wasu ke neman fakewa da wadannan al’adu domin kin tabuka kome ko kuma wani lasin na danne hakkin jama’a ba. Wannan maganar ba wata manufa ce ta shisshigin ‚yan sabon salon mulkin mallaka ba, gaskiya ce, wacce wajibi ne a fade ta kome dacinta.

Shugaban na kasar Jamus ya yaba da sabuwar alkiblar da kasashen Afurka suka fuskanta, musamman ma a karkashin shirin farfado da tattalin arzikin nan na NEPAD, inda a karo na farko baki ya zo daya tsakaninsu a game da muhimmancin rungumar tsarin demokradiyya da girmama hakkin dan-Adam da kuma daukar matakai bai daya domin samar da ci gaba mai dorewa a wannan nahiya. Wani abin madalla kuma shi ne yadda Kungiyar Tarayyar Afurka ta shigar da manufar kafa rundunar kiyaye zaman lafiya a cikin kudurorinta. Wannan wani ci gaba ne dake yin nuni ga shirin kasashen Afurka na daukar kaddararsu a hannu. Sai dai kuma ko da yake Horst Köhler yayi marhabin da sojojin da kungiyar ta tura zuwa Darfur, amma kuma ya bayyana takaicin cewar matakin ya zo a makare ta yadda aka kasa dakatar da kashe-kashe na gilla da fatattakar mutane daga yankunansu na asali da kuma fiyade da sauran ta’asar da aka sha fuskanta a wannan yanki na yammacin kasar Sudan ba. A can Cote d’Ivoire al’amura sai dada yin tsamari suke tare da barazanar ta da zaune tsaye a yankin yammacin Afurka baki daya. Yawa-yawancin rikice-rikicen dake addabar Afurka sun jibanci wata gwagwarmaya ce ta dora hannu akan albarkatun kasa, kamar yadda ake gani yanzu haka a rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a janhuriyar demokradiyyar Kongo. Wajibi ne a dauki nagartattun matakai na kandagarkin ire-iren wannan rikici. A karshe Köhler ya bayyana goyan bayansa na ganin nahiyar Afurka ta samu dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD.