1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Mali ya nada sabon Firaminista

Gazali Abdou Tasawa
December 31, 2017

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya nada Soumeylou Boubeye Maiga a matsayin sabon Firaministan kasar, kwana daya bayan da tsohon Firaminista Abdoulaye Idriss Maiga ya yi murabus. 

https://p.dw.com/p/2q9eB
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar KeitaHoto: picture alliance/dpa

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya nada Soumeylou Boubeye Maiga a matsayin sabon Firaministan kasar, kwana daya bayan da tsohon Firaministan Abdoulaye Idriss Maiga da gwamnatinsa suka yi murabus. 

Gidan talabijin na gwamnatin kasar ta Mali wanda ya sanar da wannan labari a cikin daren jiya, ya ce tuni shugaban kasar ya umarci sabon Firaministan da ya kafa gwamnati. 

Ana sa ran a wannan rana ta lahadi, Sabon Firaministan wanda ya taba rike mukamin ministan harakokin waje da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar ta Mali zai bayyana sabuwar majalisar ministocin gwamnatin. 

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai tsohon Firaministan kasar Abdoulaye Idriss Maiga ya yi murabus shi da gwamnatinsa ba tare da bayyana dalilinsa na yin hakan ba. 

Sai dai wasu rahotannin daga kasar ta Mali na cewa bayan murabus din nasa zai jagoranci yakin neman zaben shugaba Ibrahim Boubacar Keita a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.