1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya ce za a gano 'yan matan da aka sace

May 5, 2014

Shugaba Goodluck Jonathan ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin kubuto da 'yan matan da 'yan bindiga suka sace a Chibok.

https://p.dw.com/p/1BtlZ
DW_Nigeria_Integration2
Hoto: Katrin Gänsler

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin kubutar da 'yan mata 'yan marakanta 223 da ake zargin tsagerun kungiyar Boko Haram na garkuwa da su.

Shugaban ya bayyana haka a wannan Lahadi da ta gabata, yayin wata tattaunawa da manema labarai, wadda aka watsa kai tyaye ta tashoshin radiyo da talabijin. Ranar 14 ga watan jiya na Afrilu tsaregun dauke da makamai suka kai hari makarantar 'yan mata ta garin Chibok da ke Jihar Borno inda suka sace 'yan matan sama da 200. Ana nuna matukar damuwa a ciki da wajen kasar kan yadda gwamnatin Najeriya ke jan kafa na kubutar da 'yan matan.

A wani labarin, an daukaka matakan tsaro a Abuja fadar gwamnatin kasar ta Najeriya, yayin da ake fara taron tattalin arziki na Afirka cikin wannan mako.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal