1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya kori manyan hafsan hafsoshin kasar

Salissou BoukariJuly 13, 2015

A wata sanarwa da ta fitar a wannan Litinin din, fadar shugaban kasar Najeriya ta sanar cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya kori manyan hafsan hafsoshin kasar.

https://p.dw.com/p/1Fxxk
Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori babban hafsan hafsoshin kasar, da kuma sauran hafsoshi da suka hada da na sojan kasa da na sama da ma ruwan kasar. Kakakin fadar shugaban kasar ta Najeriya ne Femi Adesina ya sanar da wannan labari, inda cikin sanarwar ya ce shugaban na Najeriya ya nada Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin a matsayin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar.

Sai kuma Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai shi kuma a matsayin hafsan sojin kasa na kasar, sannan sai Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin hafsan sojojin ruwan kasar, sai kuma an nada Air Vice Marshal Sadique Abubakar a matsayin babban hafsan sojin sama. Shugaban na Najeriya kuma ya nada Air Vice Marshal Monday Riku Morgan a matsayin babban jami'in kula da bayanan sirri na tsaro a kasar sai kuma Manjo Janar Babagana Monguno da shi kuma ke a matsayin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Dama dai jama'a 'yan kasar ta Najeriya da ma na waje, na jiran wannan mataki daga sabon zabeben shugaban kasar ganin yadda wannan kasa ke fuskantar babbar matsala a fannin tsaro sakamakon ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram da kawo yanzu suka hallaka dubban rayukan al'umma a wannan kasa tare da sanya wasu dubban zama 'yan gudun hijira.