1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya yi tir da harin da ya hallaka mutane takwas

October 28, 2012

Shugaba Jonathan na Najeriya, ya ce gwamnatin kasar ta dauki matakan da su ka dace, domin kawo karshen aiyukan ta'addanci cikin kasar.

https://p.dw.com/p/16YVO
Hoto: AFP/Getty Images

Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tir da harin ƙunar baƙin wake cikin wata majami'a, a garin Kaduna da ke yankin arewacin ƙasar, wanda ya kira aikin ta'addanci. Harin ya yi sanadiyar hallaka aƙalla mutane takwas tare da jikata wasu sama da 100.

Shugaba Jonathan ya ce gwamnatin ƙasar ta ƙara zimma wajen kawo ƙarshen tashe tashen hankula da hare haren ta'addanci, tare da bayar da goyon bayan da ya dace ga jami'an, domin shawo kan matsalar.

Yanzu haka ƙura ta lafa a garin na Kaduna, inda aka ƙarfafa matakan tsaro, tare da tura jami'an tsaro cikin lunguna da kororo na birnin, amma hukumoki ba su kafa dokar hana fita ba.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas