1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Tarayyar Afirka ya isa Burkina Faso

November 10, 2014

Shugaban Kasar Mauritaniya kuma Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Mohamed Ould Abdel Aziz ya isa a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso domin tattaunawa

https://p.dw.com/p/1Dk5w
Hoto: Kenzo Tribouillard/AFP/Getty Images

Da yake magana a gaban manema labarai Shugaba Ould Abdel Aziz ya ce Tarayyar Afirka ba tazo don yin hukunci ba, amma tazo ne domin tallafawa bengarorin wannan kasa a kokarin da su ke na samun mafita. Da safkar sa a filin jirgin saman birnin Ouagadougou, shugaban na Tarayyar Afirka ya samu tarbo daga Kanar Yacouba Isaac Zida da a halin yanzu yake jagorantar kasar ta Burkina Faso kafin a samu wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar daga bangaren farar hula. A ranar uku ga watan Nowamba ce dai Tarayyar Afirka ta bai wa sojojin kasar wa'adin mako biyu na mayar da mulki ga hannun fararen hula.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo