1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen ta yi watsi da shirin zaman lafiya

Yusuf BalaSeptember 13, 2015

Mayaka da ke zama 'yan gani kashenin shugaba Abd-Rabbu Mansur Hadi na ci gaba da fafata fada da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran tun daga watan Maris.

https://p.dw.com/p/1GVm5
Jemen Plakat Präsident Mansour Hadi
Shugaba Mansour HadiHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban kasar Yemen da ke gudun hijira a Saudiyya ya bayyana a ranar Lahadin nan cewa babu hannunsa cikin tattaunawar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani a rikicinsu da mayakan 'yan Houthi, wani abu da ke neman gusar da hasashen samar da zaman lafiya a wannan kasa da ta shiga yakin basasa sama da watanni biyar.

A cewar majiyar gwamnatin ta shugaba Hadi ba za ta shiga duk wata tattaunawa ba wacce 'yan tawayen za su ki mutunta yarjejeniyar kasa da kasa mai lamba 2216 su kuma gindaya wasu sharuda.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dai bukaci dukkanin bangarorin biyu da su ajiye duk wasu sharuda da suke gindayawa wadanda ba za su taimaka ba a kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiyar. Zaman tattaunawar da aka yi dai a watan Yuni ya gaza nasarar kawo karshen tashin hankalin da ya jawo asarar rayukan sama da mutane 4500 da sanya kasar ta Yemen cikin yanayi na yunwa.