1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun fara taron koli a birnin Accra na kasar Ghana

July 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuHN

An bude taron kolin kasshen kungiyar tarayyar Afirka AU a birnin Accra na kasar Ghana. Muhimmin batun da zai mamaye zauren taron na yini 3 wanda ke samun halarcin shugabanni 53 na Afirka dai shi ne karfafa hadin kai tsakanin kasashen Afirka. Shugaban Libya Muammar Ghaddafi ya dade ya na neman a kafa wata hadaddiyyar kasar Afirka guda daya. Shugaban AU Alpha Omar Konare wanda yayi jawabin bude taron ya yi kira ga MDD da ta zartas da wani sabon kuduri da zumar kawo karshen rikicin lardin Darfur da ke yammacin Sudan. Ya ce ko da yake Sudan ta amince da girke rundunar hadin guiwa ta MDD da kungiyar AU a Darfur amma aikin rundunar ka iya gurguncewa saboda rashin kudi da kuma wani karsashi na siyasa. Sauran batutuwan da taron zai mayar da hankali kansu sun hada da rikicin Somalia, Chadi da Ivory Coast da kuma dambruwar siyasa a Zimbabwe.