1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin APC sun dira a jihar Rivers

November 6, 2013

Yayin da jam'iyyar APC ke ci gaba da zawarcin bijirarrun jam'iyyar PDP, sun isa Fatakol, inda suka gana da gwamna Rotimi Amaechi a yunkurin jawo shi cikinsu.

https://p.dw.com/p/1AClA
Treffen nigerianischer Gouverneure. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja
Hoto: DW

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta gayyaci bangaren sabuwar jam'iyyar PDP a Jihar Rivers, don hadewa a yi tafiya daya domin kafa sabuwar gwamnati a Najeriya. Sai dai daga furuce-furuce da aka yi a gurin wannan taro, da alama adawar siyasa a Najeriya tana kara zafafa.

Bayan bude taro da kade-kade da raye-raye, da suka gudana a cikin harabar gidan gwamnatin Jihar ta Rivers, inda dubban magoya baya suka halarta. Akwai jawabai da gaggan 'yan jam'iyyar ta APC suka gabatar. Daga masu jawaban akwai Bola Ahmad Tinubu da ya bayyana takaicin dalilan da ya sa taron bai gudana a wannan Litinin (04. 11. 13) ba, kamar yadda aka tsara, sai wannan Talatar (05. 11. 13) .

Gen. Muhammadu Buhari, presidential candidate of the Congress for Progressive Change, attends a campaign rally in Lagos, Nigeria, Wednesday, April 6, 2011. Buhari, a former military ruler of Nigeria, has gained support in his third bid to become president of the oil-rich nation. Buhari ruled Nigeria from 1983 to 1985 after a military coup deposed the elected president. (AP Photo/Sunday Alamba)
Janar Muhammadu BuhariHoto: AP

Ya ce "Ba ma son tashin hankali ko yamutsi, so muke mu zo jihar Rivers cikin kwanciyar hankali, don mu sadu da kowa a nan, bisa neman hadin kanku a tafiyar siyasa tare. Shi ya sa muka ce a samu nutsuwa, muka daga taron sai yau Talata"

Taron dai, na neman hadin kan jihohin da gwamnonin PDP bakwai da ke yi wa uwar jam'iyyarsu tawaye, don su shiga jam'iyyar APC a yi tafiya tare a siyasar 2015.

Bayan dai gabatar da jawabi cikin Turanci da shugaban tawagar ta jam'iyyar APC, wato Janar Muhammadu Buhari ya yi, inda ya nemi jama'ar jihar Rivers su shigo a yi tafiya tare, Janar din ya kara wa wakilinmu Muhammad Bello bayani, kan zabubbukan kasar

Buhari ya ce "babban abin shi ne a tabbatar an yi zabe kan ka'ida don duk abin da muke yi ba za a bari ayi zaben ba, zuwa za ai a rubuta, aje gidan rediyo a fadi, ace in mutum yana da magana ya tafi wurin shari'a, to abin ba zai yi wu ba. Saboda haka wannan ya danganta ga 'yan Najeriya, dukkansu su tabbatar sun zabi wadanda suke so su wakilce su, su kuma shugabance su"

Da yake mayar da jawabi a maimakon jama'ar jihar Rivers, Gwamna Rotimi Amaechi, ya fara da yin jawabin na hannunka mai sanda , inda yace.

Senator Lawali Shuaibu, General secretary ANC party. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa aus Abuja in Nigeria
Lawali Shuaibu, jigo a jam'iyyar APCHoto: DW/U. Musa

"Kamata ya yi mutum ya san cewar in har ka yarda da Ubangiji, to babu kuma shayin wani. Kuma an sha za a cire ni daga gwamna, tun shekara ta 2007, amma har yau ina nan daram"

Daga karshe dai Gwamna Amaechi ya nunar cewar ya ji gayyatar ta jam'iyyar APC, kuma za a yi shawara da jama'ar Rivers da kuma gwamnoni bakwai na kasar, kafin yanke hukunci.

Wannan taro dai da aka yi kusan kukan kurciya ne, tare kuma da fitowa karara don yin adawa da fadar gwamnatin Najeriya, a daya daga zuciyar jihohin yankin Niger Delta, inda shugaba Goodluck Jonathan ya fito. Masu sharhin siyasa na hangen cewar, labudda akwai kallo ga mai yawan rai a siyasar 2015, bisa la'akari da yadda adawa ke dada ruruwa daga yankin da shugaban kasar ya fito.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani