1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar Taiwan ta isa Amirka duk da gargadin China

March 30, 2023

Duk da gargadin da China ta yi wa Amirka, shugabar ta Taiwan ta yada zango a New York a kan hanyarta ta zuwa kasashen Gwatemala da Belayis da suka amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

https://p.dw.com/p/4PTSH
Hoto: Yuki Iwamura/AP/picture alliance

Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta sauka a birnin New York na Amirka a daidai lokacin da China ke kurarin daukar mataki tsattsaura idan har kakakin majalisar wakilan Amirka Kevin McCarthy ya yarda ya gana da ita.

Tuni dai ofishin jakadancin China da ke Amirka ya sanar da cewa ya yi magana da wasu manyan jami'an Washington, inda ya gargade su cewa idan har suka tarbi shugabar ta Taiwan tamkar sun togali China ne ta hanyar yin hannun riga da manufofinta. Duk da cewa kawo yanzu hukumomin Amirka ba su mayar da martani kan wannan gargadin ba, amma wasu rahotanni na cewa tuni shiri ya yi nisa kan yadda shugabar ta Taiwan za ta gana da kakakin majalisar wakilan Amirkan a birnin California.

China dai na ikirarin Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta, yayin da ita kuma Taiwan ta jima tana cewa ita kasa ce mai cin gashin kanta, lamarin da ke sanya hukumomin China fusata a duk lokacin da wata kasa ta ketare ta nuna gamsuwa da 'yancin na Taiwan.