1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sihle Tshabalala- daga dan daba zuwa dan sauyi na gari

Julia Jaki/ ASSeptember 23, 2015

Yayin da mahukuntan Afirka ta Kudu ke kokawa kan yawaitar aikata miyagun laifuka musamman tsakanin matasa, wasu al'ummar kasar sun dau aniyar fidda hanyoyin magance wannan matsala.

https://p.dw.com/p/1Gbly
Videostill von BENG150901_152_AOMSASIHLE_01C
Hoto: DW

Da dama daga cikin al'ummar Afika ta Kudu dai sun yanke shawarar fitar wa kansu kitse daga wuta musamman ta bangaren magance miyagun laifuka tsakanin matasa. Sihle Tshabalala wanda a baya ya yi zaman gidan kaso sakamakon laifukan da ya aikata a baya na fashi da makami na daga cikin wanda suka tashi haikan da taimakon kungiyoyi masu zaman kasu wajen magance wannan matsala.

Dan shekaru 32, Sihle na zaune ne a kauyen Langa na kasar ta Afirka ta Kudu. Mutum ne da ake ganin girmansa a kauyen duk kuwa da irin tsarin rayuwar da ya dauka a baya. A zantawarsa da DW, Sihle ya ce rashin fuskantar alkibla ta gari bayan kammala karatun sakandare ne ya sanya shi shiga mummunar ta'ada.

Videostill von BENG150901_152_AOMSASIHLE_01C
Hoto: DW

"Bayan kamala sakandare ban yi tunanin zuwa jami'a ba, kawai sai na fara yin fashi da makami. Lokacin da na cika shekara 18 na mallaki motocin hawa biyu sannan na kama gida a unguwar masu kudi kana ina sa kaya masu tsada da kuma yin rayuwa irin ta kasaita. Ina shekara 19 ne aka kama ni aka daure ni tsawon shekaru 11."

Alkibla ta gari don zama na-gari

A lokacin da ake masa shari'a gabannin kai shi gidan yari, Sihle ya yi tunanin sauya rayuwarsa. Mutumin kuwa ya yi wannan karatun ta nutsun ne saboda irin halin da ya tsinci kansa a ciki don haka sai ya yanke shawara ta bin tafarki na gari don amfana wa kansa da ma sauran jama'a wani abu.

"Na fahimci cewar zan yi zaman jarun na shekaru shida ko bakwai, ko ma goma in har ban zama na gari ba. Wannan ne ya sanya ni tunanin sauya tsarin rayuwa ta saboda haka sai na fara koyar da darasin lissafi da na turancin Ingilishi a gidan yari."

Tallafi don magance zaman banza

Bayan da Sihle ya fito daga gidan yari, bai yada wannan kyakkyawan aiki na karantarwa da ya fara lokacin da yake daure ba. Hasali ma hada karfi yayi da wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “Brothers for All” wadda ta dafa masa wajen koyar da matasa fannonin karatu da dama ciki kuwa har da na ilimin na'urar kwamfiyuta.

Videostill von BENG150901_152_AOMSASIHLE_01C
Hoto: DW

Zoko Ngoma mai shekaru 25 na daga cikin irin daliban da Sihle ke karantarwa. Shi ma dai kamar Sihle ya yi zaman jarun har na shekaru biyar saboda fashi da makami da ya yi. A hirarsa da DW, matashin ya ce wannan aiki da Sihle ke yi abin a yaba ne kuma nan gaba yana tunanin yin koyi da shi.

"Da na fito daga gidan yari na aika wa kamfanoni da ma'aikatu da dama takardar neman aiki. Wasu sun neme ni saboda cancanta ta amma saboda na taba aikata laifi ba su dauke ni ba. Wannan yanayi ya sanya ni tunanin yin irin abinda Sihle ya runguma yanzu."

Yanzu haka dai daliban dai na maida hankali wajen koya kuma har ma wasu kimanin mutum 170 na son shiga a dama da su a irin darussan da Sihle ke karantarwa don yin amfani da irin ilimin da za su samu wajen neman na kansu.