1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: An samar da tudun na tsira a Homs

Ahmed Salisu
August 3, 2017

Wata yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da 'yan tawaye ta fara aiki a yau din nan bayan da gwamnatin Rasha ta shiga tsakani har aka kai ga samun tudun na tsira.

https://p.dw.com/p/2hdtb
Homs Rebellen Evakuierung 09.05.2014
Hoto: Reuters

An dai amince da arewacin birnin Homs ne ya kasance tundun na tsira din kuma a halin yanzu wannan waje ya kasance irinsa na uku da aka samar a kasar ta Siriya wadda ta shafe shekaru da dama ta fama da yaki. Masu aiko da rahotanni suka ce tun bayan fara aiki da wannan yarjejeniyar da misalin karfe 9 na safiya agogon GMT aka daina jin amon bindigogi har ma mazauna wannan yanki suka ce hankula sun fara kwanciya. Yanzu haka dai jami'an tsaro musamman ma dai 'yan sanda za su sanya shingaye na binciken ababan hawa a gobe Juma'a domin tabbatar da tsaro kana wani kwamiti da zai kunshi bangaren gwamnati da na 'yan tawaye zai yi aiki don tabbatar da cewar yarjejeniyar ta dore.