1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya sun samu nasarar fatattakar 'yan IS

Lateefa Mustapha Ja‘afarMarch 2, 2015

Dakarun kasar Siriya sun ce sun samu nasarar kwato wasu kauyuka 32 daga hannun kungiyar 'yan ta'addan IS a arewa maso gabashin gundumar Hasakeh.

https://p.dw.com/p/1Ek2c
Hoto: REUTERS/H. Katan

Hakan ya zo ne a kokarin da dakarun na Siriya ke yi na kwato babbar hanyar da ta hada babban birnin gundumar ta Hasakeh da kuma garin Qamishli da ke kusa da kan iyakarsu da Iraqi da kuma Turkiya. Ko da yake shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya Rami Abdel Rahman ya tabbatar da cewa dakarun gwamnatin sun samu nasara a kan 'yan ta'addan na IS, sai dai yace kauyuka 23 ne suka kwato daga hannunsu ba 32 ba kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya SANA ya ruwaito. A hannu guda kuma kungiyar kare hakkin dan Adam din ta ce dakarun Kurdawan kasar Iraqi ma na yakar kungiyar ta IS domin kwato kauyen Tal Tamr da ke kudu maso yammacin gundumar ta Hasakeh.