1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Gambiya: Wane zabi ya rage wa ECOWAS?

Uwais Abubakar Idris MNA
January 16, 2017

Bayan da ECOWAS ta gaza shawo kan Jammeh na ya amince da shan kaye, shin wane mataki za a dauka kanshi?

https://p.dw.com/p/2Vsth
Gambia Präsident Yahya Jammeh
Hoto: Reuters

Rushewar duk wani kokari na bin hanyar diplomasiyya ga shugaban na kasar Gambiya mai barin gado da ke kare makalewa a gadon mulkin kasar, na haifar da yanayi  mai wahalar gaske ga kungiyar ECOWAS, wacce bayan zarya sau biyu zuwa kasar har yanzu shugaban na Gambiya Yahya Jammeh na nuna ba gudu ba ja da baya a kan batun ya amince da zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disambar bara.

Wannan yanayi ya bar kungiyar da zabi na karshe da tun da farko ta ambata na amfani da karfin soja wajen kakkabe Yahya Jammeh daga mulkin kasar, domin tabbatar da abin da suka kira tabbatar da dorewar mulkin dimukuradiyya a kasar. Ko da yake sun ambata hakan har zuwa wannan lokaci sun yi bakam a kan hakan, ko kuwa dai suna nuna ja da baya ba tsoro ba ne? Dr Kole Shattima masanin kimiyyar siyasa ne a Najeriya da kasashen Afirka na mai bayyana cewa.

"Yanzu dai muna cikin tsaka mai wuya kenan. Wannan matsalar da muka samu da nike ganin cewa idan ita kungiyar ECOWAS ba ta fito ta nuna karfin ikonta ba, a nan gaba idan irin wannan abin ya faru, zai kasance ba ta da kima. A gefe guda idan aka yi amfani da sojoji ba mu san irin abin da zai faru ba, domin ai sojojin sun nuna cewa suna goyon bayan kasarsu."

Neman amincewar Gamaiyar Kasa da Kasa

A yayin da tuni kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana cewa daga ranar 19 ga watan nan na Janairu, ba za ta dauki Jammeh a matsayin shugaban Gambiya ba, tuni dai kungiyar ta tuntubi Majalisar Dinkin Duniya tare da neman amincewa ta yi amfani da karfin soja muddin aka yi kokarin hana rantsar da zababben shugaban kasar Adama Barrow.

Gambia Adama Barrow gewählter Präsident
Shugaba mai jiran gado Adama BarrowHoto: picture-alliance/AA/X. Olleros

Ga kunyoyin kare hakin jama'a na neman a ci gaba da bin hanyar lalama wajen shawo kan lamarin domin kauce wa hatsarin da ke tattare da amfani da karfin soja a kasar. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar fararen ta kasashen Afirka ta Yamma.

"Ba ma son ya zama cewa an yi amfani da karfin soja a sake kawo yanayin da zai sanya talakawa a cikin mummunan hali. Don haka in har aka matsa mashi ta hanyar diplomasiyya da tattalin arziki, aka toshe hanyar samun tallafi ga kasar ba zai kai labara ba."

To sai dai Dr Kole Shattima na ganin akwai mafita daga wannan rikicin siyasa na Gambyia da ke kara murtukewa.

Abin jira a gani shi ne abin da ka iya faruwa nan da ranar Alhamis mai zuwa ga Shugaba Jammeh, domin da alamun sannu a hankali ruwa na kare wa dan kada.