1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Kenya ta mamaye Jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
November 2, 2017

A wannan makon dai jaridun Jamus sun mayar da kankali ne kan rikicin siyasar kasar kenya, da rikicin kasar Sudan ta Kudu da ma kasar Kwango.

https://p.dw.com/p/2mwKk
Kenia Präsidentschaftswahl Wahlsieger Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a yayin da hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben zagaye na biyuHoto: Reuters/T. Mukoya

 

Za mu soma ne da jaridar Süddeutsche Zeitung  wacce ta buda labarinta da rikicin siyasar kasar kenya, inda jaridar ta ce, duk da irin fargaban da ake yi, an gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya. Inda jaridar ta ce, kotun kundin tsarin mulkin kasar ta gaza yin wani abu, domin ya nuna cewa ba ta da halin sauraron karan da aka shigar na dage zaben. Babban alkalin kotun David Maraga ya nemi afuwa, yayin da sanar cewa biyu ne kacal daga cikin alkalai bakwai da yakamata su yi zama sauraron shari'ar suka samu halarta, yayin da alakli daya ke kasar waje yana jinya, daya alkalin kuma bai samu jirgin sama da zai kawo shi Nairobi babban birnin kasar ba. kana alkalai biyu sun tsame kansu daga shari'ar yayin da mataimakiyar babban alkalin kotun ta nuna rashin iya halartan zaman kotun, bisa raunata mai tsaron lafiyarta da aka yi yayin wani hari da aka kai mata ranar Talata jajibirin zaman sauraron shari'ar.

Sai jaridar die Welt, wace ta duba rikicin kasar Sudan ta Kudu, jaridar ta bada misali ne ga wata mata mai suna Blessing, mai dauke da juna biyu tana goye da jariri a bayanta, ga wasu yaran a hannunta. a cewar jaridar wadannan iyalan sun kwashe kwanaki biyar suna tafiyan kafa, inda da ganinsu kasan sun galabaita.

Jamhuriyar Demokradiyar Kwango it ce kasar Afirka mafi yawan shinfidadden arzikin ma'adinan karkashin kasa. Wannan shi ne labarin jaridar die Zeit. Kasar Kwango dai na samun makuden kudi ta wannan arzikin karkashin kasa, inda jaridar ta bada misalin cewa kamfani daya na kasar Kanada ya biya Kwango haraji na dalar Amirka miliyan 60, wanda za a ce babban kudi ne da za su taimaka wajen inganta rayuwar 'yan kasar wadanda ke rayuwa a kasa da dala 500 a shekara, sai dai kaico duk irin wadannan kudadaden da ake biya sakamakon ma'adinai da ake hakowa, suna karewane a aljifen jami'an gwamnati da ke karban haraji, yayin da talakawa ke fama da talauci da yake-yake.