1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soja da 'yan Biafra sun gwabza a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
September 11, 2017

A cewar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra daga Najeriya mambobinta biyar ne suka mutu bayan da suka gwabza da jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/2jh3e
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Masu fafutikar 'yancin Biafra a Najeriya sun gwabza fada da dakarun sojan kasar a Kudu maso Gabashin Najeriya a ranar Lahadi, inda ake zargin mutane biyar sun halaka, ko da yake jami'an tsaro a Najeriyar sun karyata wannan zargi.

A cewar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra daga Najeriya mambobinta biyar ne suka mutu bayan da suka gwabza da jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da 'yan sanda a kokarinsu na kama Shugaban kungiyar wato Nnamdi Kanu a gidansa da ke garin Umuahia.