1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Kamaru sun kashe 'yan aware 24

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2020

Sojojin gwamnatin Kamaru sun sanar da kashe mayakan 'yan awaren yankin da ke magana da Turancin Inglishi su 24 a wasu jerin hare-hare da suka kai a mabuyarsu a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/3dxf8
Kamerun Amchide Armee Soldaten Anti Boko Haram 11/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Sojojin gwamnatin Kamaru sun halaka mayakan kungiyar 'yan awaren yankuna masu magana da Turancin Inglishi na yankin Arewa masu yammacin kasar guda 24, a wasu farmaki biyu da sojojin suka kai a baya bayan nan a mabuyar 'yan awaren.

 Janar Valere Nka babban hafsan sojan kasar ta Kamaru a yankin na rainon Ingila ne, ya sanar da hakan a wata fira da ya yi da gidan radiyo da Talabijin na kasar ta Kamaru a yammacin talatar da ta gabata.

Janar din ya ce sojojin gwamnatin sun halaka 'yan awaren 13 a farmakin farko da suka kai a garuruwan Bali da Batibo da Widikum, inda 'yan awaren suka datse babbar hanyar da ke zuwa Najeriya, a yayin da suka kashe wasu 'yan awaren 11 a farmaki na biyu da suka kai a garin Mbokam inda suka yi nasarar kama tarin makamai. Sai dai kuma babban sojin kasar ta Kamaru bai bayyana ranaikun da sojojin Kamarun suka kaddamar da wadannan hare-hare ba.