1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji na ci gaba da hare-hare a biranen kasar Cote d'Ivoir

Salissou Boukari
May 15, 2017

Rahotanni daga birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoir na cewa, ana ci gaban da fuskantar borin sojoji a birnin Bouake da ke arewacin kasar, da kuma Abidjan babban birnin kasar, inda sojojin masu bore suka kafa shingaye.

https://p.dw.com/p/2d0B3
Elfenbeinküste Soldatenmeuterei
Sojoji masu bore a kasar Cote d'IvoirHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wani mai magana da yawun sojojin da ke bori a birnin Abidjan ya sanar a wannan Litinin din cewa, tattare hanyoyi da suka yi, da kuma harbe-harben da suke yi ba juyin mulki ba ne, illa kawai nuna buktar su ta a biya su kudadansu kamar yadda shugaban kasar Alassane Ouattara ya rattaba hannun cewa zai biya su.

A ranar Alhamis ce dai da ta gabata wani mai magana da yawun sojojin da suka yi bori a kasar ya nemi gafara a gaban Shugaban kasar Alassane Ouattara dangane kan borin da suka yi a baya, inda kuma ya sanar cewa sun yi watsi da dukannin bukatunsu na neman a biya su wasu kudaden na alawus, sai dai kuma ga dukkan alamu wannan mataki bai yi wa saurau sojojin dadi ba.