1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun karbe ragamar mulki a kasar Zimbabuwe

November 15, 2017

Rundunar sojin kasar Zimbabuwe ta ce shugaba Mugabe da iyalansa su na cikin koshin lafiya da kuma kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/2neEN
Zimbabwe Soldaten vor Harare
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Sojoji a Zimbabuwe sun karbe ikon ragamar mulkin kasar. Kungiyar tsoffin sojojin kasar, ta yaba da matakin da dakarun sojin kasar suka dauka na karbe ikon gidan rediyon gwamnatin kasar, ta na mai cewa hakan mataki ne na gyara ba tare da zubar da jini ba.

Shugaban tsoffin sojojin Chris Mutsvangwa ya fada a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu cewa babban hafsan sojin Zimbabwe Janar Constantino Chiwenga ya yi aikin da zai samarwa kasar tafarkin demokuradiyya ta gari. A sakon da ta aike wa al'umar Zimbabuwen, rundunar sojin kasar ta ce shugaba Mugabe da iyalansa na cikin koshin lafiya. 

Simbabwe Constantine Chiwenga und Robert Mugabe
Hoto: Getty Images/AFP/A. Joe

Rundunar sojin ta kuma musanta cewa juyin mulki ta yi. Ta ce sun zo ne domin gyara kuma za su mayar da kasar kan tafarkin dimokuradiyya da zarar komai ya daidaita. Cikin wani kashedi da ya yi a ranar Litinin, babban hafsan hafsoshin kasar ta Zimbawe, ya soki matakin korar mataimakin shugaban kasar ta Zimbabwe daga mukaminsa, inda ya sha alwashin cewa sojoji ba za su zuba idanu suna kallo ba, idan har ba a dakatar da dauki dai-dai da ake yi da 'yan jam'iyyar ta Zanu-PF mai mulkin kasar tun daga shekara ta 1980 ba.

Tuni ma dai manyan kasashen duniya suka yi kira ga 'yan kasashen nasu dake Zimbabuwe, da su natsu wajen guda, saboda halin da kasar ta shiga. Tsohon mataimakin shugaban kasar ta Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, mai shekaru 75 da haihuwa da ake tunanin zai gaji kujerar ta Shugaba Mugabe, an sauke shi ne daga mukaminsa a makon da ya gabata, kuma tuni ya tsere ya bar kasar.